Shekarar 2021: Hotunan yadda aka yi shagalin shiga sabuwar shekarar 2021 a faɗin duniya

Bayanan bidiyo, Biidyon yadda aka yi bikin sabuwar shekara a wasu sassan duniya
An wallafa

Miliyoyin mutane a fadin duniya sun shaida yadda aka yi ban-kwana da shekarar 2020 da kuma murnar shigowar sabuwar shekara ta 2021, ko da yake annobar cutar korona ta tilastawa da dama gudanar da bikin a kulle cikin gidajensu.

Sakamakon kullen korona ko sauran dokokin da kasashe da dama suka shimfida, an umarci masu fita yin dabdala da su kasance duk a cikin gidajensu.

Wasu sun halarci bukukuwan sanye da takunkumi ko kuma wasu matakai na yin taka tsan-tsan.

A birnin Tokyo (hoton da ke ƙasa), mutane sun ziyarci wurin ibada na Kanda Myojin Shrine don gudanar da addu'oi.

Sanannen wurin ibadar na Shinto ya zaftare yawan masu ziyarar da ya kamata su shiga, yayin da kasar ta Japan ke fuskantar sabuwar barazanar ƙwayar cutar korona.

Wearing masks, people in Tokyo visit the Shinto Kanda Myojin Shrine to mark the new year

Asalin hoton, Getty Images

A birnin Wuhan na ƙasar China, dandazon jama'a sun hallara dauke da balan-balan da tufafi na kawa don duban lokaci zuwa tsakar dare a jajiberin sabuwar shekara.

People attend New Year bell-ringing ceremony in front of Hankow Customs House during New Year's Eve celebrations on 31 December 2020 in Wuhan, Hubei Province of China

Asalin hoton, Getty Images

Tartsatsin wuta ya haske sararin sama a kasar Taiwan don bikin shiga sabuwar shekarar 2021, yayin da birane da dama suka soke gudanar bukukuwan, a maimakon haka aka mayar da gudanarwa ta yanar gizo.

Fireworks are launched from the Taipei 101 commercial building to celebrate the New Year in Taipei on 1 January 1 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Kamar wadannan iyalai a birnin Seoul, Korea ta Kudu, da dama a fadin duniya sun gudanar da bukukuwan ne a gajarce cikin gidajensu.

One family in Seoul lit a candle and shared a cake to start 2021

Asalin hoton, Getty Images

A kasar Philippines, wasu sun taru a dandalin shaƙatawa a birnin Manila (hoton da ke ƙasa) don kallon wasan wutar. Mahukunta sun umarci mazauna yankin da ka da su cunkusu wuri guda.

Small groups gathered in the main square in Yekaterinburg, Russia

Asalin hoton, Getty Images

A yankin Hong Kong, jama'a sun taru a bakin gaɓar tekun 'Victoria Harbou' don gudanar da bukukuwan tare.

New Year's Eve fireworks erupt over Ras al-Khaimah, one of the world's largest fireworks shows on 1 January 2021.

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da kuma a Hadaddiyar Daular Larabawa, daya daga cikin wuraren da aka shaida kayatattun launukan wasan wuta na sabuwar shekara da suka haske sararin saman dandalin Ras al-Khaimah...

Fireworks on the Burj Khalifa tower in Dubai during the new year's eve celebrations on December 31, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Tartsatsin wuta ya mamaye sararin sama a kewayen gini mafi tsawo a duniya Burj Khalifa, bayan da agogo ya buga ƙarfe 12 na tsakar dare a Dubai.

Fireworks explode over Berlin's landmark Brandenburg Gate to usher in the new year during a concert 'Willkommen 2021' (Welcome 2021)

Asalin hoton, Getty Images

Waɗannan masu ibadar a Abuja, babban birnin Najeriya sun shiga sabuwar shekarar ne ta hanyar yin ibada a coci.

Worshippers attend the end of the year service at Dunamis International gospel centre in Abuja, Nigeria, 31 December 2020

Asalin hoton, Reuters

A can ma Abidjan babban birnin Ivory Coast, mutane sun samu damar kalon wasan tartsatsin wuta tare da ƴan uwa da abokan arziƙi.

Ivorians watch a fire works display to ring in the New Year, in Koumassi a neighbourhood of Abidjan on 1 January 2021

Asalin hoton, Getty Images

Amma a birnin New York na Amurka, mutane kaɗan ne aka bari suka shiga dandalin Times Square don kallon bikin shiga sabuwar shekarar.

A woman throws confetti during the 2021 New Year's Eve celebrations on 1 January, 2020 in New York City

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomin Brazil sun rufe gaɓar tekun Copacabana Beach, a birnin Rio de Janeiro, amma hakan bai hana mutane more bikin ranar ba.

People enjoy of the end of the year celebrations at Copacabana beach in Rio de Janeiro, Brazil, 31 December 2020.

Asalin hoton, EPA

An gudanar da wasaun tartsatsin wuta a fadin birnin London. Jirage marasa matuka sun cika sararin samaniyar a kusa da wurin shakatawa na 02 Arena a gabashin birnin London suna nuna sakonni da suka danganci annobar korona, da suka hada da alamar hukumar inshorar kiwon lafiya ta kasar NHS.

Fireworks and drones illuminate the sky in London

Asalin hoton, PA Media

2px presentational grey line

Dukkan hotunan na da haƙƙin mallaka