Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Loujain al-Hathloul: An yanke wa ƴar fafutukar Saudiyya hukuncin ɗaurin shekara 5 a gidan yari
An yanke wa sananniyar mai fafutukar kare haƙƙin mata ta ƙasar Saudiyya, Loujain Al-Hathloul hukuncin ɗaurin fiye da shekara biyar a gidan yari, a bisa zargin ''ta'addanci.''
Da ma dai Loujian, mai shekara 31 ta shafe shekara biyu da rabi a tsare a gidan yarin da aka tsaurara wa matakan tsaro.
Ita da sauran wasu masu fafutukar ne aka tsare a shekarar 2018 kan zarge-zarge da suka haɗa da na yin mu'amala da ƙungiyoyin da ba sa ga maciji da juna da ƙasar ta Saudi Arabia.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama na ƙasa da ƙasa sun sha yin kiraye-kiraye da a sako ta.
Amma a ranar Litinin ne kotun musamman mai hukunta masu masu aikata manyan laifuka ta ƙasar da aka kafa don yin shari'a ga masu aikata laifin ta'addanci ta yanke mata hukunci kan tuhume-tuhume da dama da suka haɗa da yunƙurin yin karan tsaye ga harkokin tsaron ƙasar da kuma yada manufofin ƙasashen waje.
Ta kuma yanke mata hukuncin ɗaurin shekara biyar da wata takwas a gidan yarin. An kuma bayyana dakatar da hukuncin shekaru biyu da watanni takwas ɗin da ta shafe a tsare.
Ita da danginta sun musanta duka zargin da ake yi mata. Sun kuma ce an azabtar da ita a gidan yarin - zargin da ƙasar ta yi watsi da shi.
An tsare Hathloul makonni kafin a amince wa matan Saudiyyar suka riƙa tuƙin mota a shekarar 2018 - wanda wannan na daga cikin fafutikar da Ms Al-Hathloul ɗin da wasu da aka kama suka daɗe suna neman a tabbatar.
Mahukuntan Saudiyyar sun dage a kan cewa tsare ta da aka yi bas hi da nasaba da batun.
Y'an uwan Hathloul sun ce an kuma haramta mata magana da kowa har na tsawon watanni uku bayan cafke ta, sa'annan an riƙa gana mata azaba da wutar lantarki, bulala da kuma cin zarafi ta hanyar lalata.
Sun kuma yi zargin cewa an yi mata tayin samun ƴanci muddin ta amince ta faɗi cewa ba a azabtar da ita ba.
Masu rajin kare haƙƙin bil'adama sun ce shari'ar da aka yi mata ba ta kan hanyar bin ƙa'idojin ƙasa da ƙasa.
A watan Nuwamba ne, ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da mayar da da ita kotun musamman ta masu aikata manyan laifuka, tana mai cewa hakan ya bankaɗo ''cin zali da munafunci'' na mahukuntan ƙasar ta Saudiyya.
Ana dai kallon wannan shari'a a matsayin wadde za ta kara zubar da ƙimar Yarima mai jiran gado na Saudiyyar, Mohammed Bin Salman, wanda ake ganin yana yawan janyo cece-kuce.
Ya jagoranci shirin yin garanbawul da suka haɗa da ɗage takunkumin hana mata tuƙi.Amma kuma an sha sukar lamirinsa kan ci gaba da cafke masu fafutukar kare hakkin bil adama, da kuma rawar da mahukuntan kasar ta Saudiyya suka taka wajen kisan ɗan jaridar nan Jamal Khashoggi.
Sharhi daga Lyse Doucet (Babbar Wakiliyar BBC ta Ƙasa da Ƙasa)
Yanzu Loujain Al-Hathloul ta ƙara zama shahararriya saboda azabtar da itan da aka yi fiye da a lokacin da ta kasance a faggen nuna jarumta a fafutikar da ta ke yi.
Ta ƙara fito da cin zarafin bil'adama a fili da ya yi katutu a cikin tsarin manufofin yin garambawul ga tattalin arziƙi da zamantakewar Saudiyya - yayin da ta ke ƙara tsaurara ƙarfin ikonta kan harkokin siyasa.
Lokacin da Joe Biden zai kaɓi ragamar shugabancin Amurka, ana sa ran ya ɗauki matakai masu tsauri kan cin zarafin bil'adama.
Amma mahukuntan Saudiyyar sun jajirce a kan cewa za su ci gaba da tsayawa a kan matsayin abin da suka sa a gaba.
Ƙasar ta yi amanna a matsayinta na ƙasa mafi girma a fannin fitar da man fetur da kuma matsayinta na yankin, na da muhimmanci ga ƙasashen yammacin duniya fiye da kowa.
Hukuncin da aka yanke wa Al-Hathloul, da ya haɗa da shekarun da aka soke bayan ta shafe su a tsare, na nufin za a iya sakin ta a cikin sabuwar shekara.
Hakan zai taimaka wajen sassauta matsin lamba kan Saudiyyar, wadda ba ta son a riƙa yi mata kallon tana bin abubuwan duk abin da wasu ƙasashe suka shimfiɗa mata.