Lafiya Zinariya: Kashi na biyu na hira da mai cutar HIV kan yadda shan magunguna ke sauya rayuwar masu cutar

Bayanan sautiKashi na biyu na duba kan yadda shan magungunan cutar HIV ke sauya rayuwar masu dauke da cutar.
An wallafa

Latsa hoton da ke sama don sauraron shirin:

Cutar Aids kan samu ne idan kwayar cuta ta HIV ta shiga jikin mutum ta raunana garkuwar jikinsa. Idan garkuwar jiki ta yi rauni, mutum zai yi saurin kamuwa da wasu cutukan Kaman cutar TB da wasu nau'ukan daji.

Ana kammuwa da cutar HIV ne ta hanyar saduwa ko ta jini. Misali amfani da allura ko reza ko wani abu mai tsini da mai dauke da cutar ya yi amfani da shi ya yanke. Ko ta rauni ko a jiki.

Sai dai a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita.