A Faɗa a cika: Abin da ke haifar da ciwon ƙoda a Yobe - Maimala Buni

Gwamna Maimala Buni
Bayanan hoto, Gwamna Maimala Buni ya ce ya cika da dama daga alkawuran da ya dauka
An wallafa

Gwamnan jihar Yobe ya ce bincike na farko-farko da masana suka gudanar ya nuna cewa ruwan sha na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da yawaitar masu fama da ciwon koda a jihar.

Yobe na a sahun gaba a jihohin da suka fi yawan masu kamuwa da cutar koda a Najeriya.

A lokacin tattaunawa ta awa guda cikin shirin A FADA A CIKA wanda BBC ke shiryawa da tallafin gidauniyar MacArthur, Gwamna Mai Mala Buni ya ce an kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Farfesa Maimuna Waziri domin yin bincike da gano musabbabin ciwon.

A cewar sa ana gudanar da binciken ne da hadin gwiwar ofishin jakadancin Amurka a Najeriya.

Tun farko dai mutane biyu wadanda suka halarci tattaunawar da BBC ta shirya da gwamnan, wato Bulama Bukarti da kuma Sulaiman Kachalla sun bukaci gwamnan da bayyana kokarin da gwamnatin jihar ta Yobe ke yi na ganin ta magance yawaitar kamuwa da cutar koda a jihar.

Baya ga batun bincike kan ciwon koda shirin ya kuma tattauna a kan bangarori da dama, daga cikin su akwai na gyaran ilimi, da kuma yadda gwamnan ke hada aikinsa na gwamna da kuma shugabantar jam'iyyar APC a kasa baki daya.

Gwamnan ya ce an samu ci gaba a yawan dalibai da suke yin nasara a jarrabawar fita daga babbar sakandare.

Sai dai kuma duk da haka kasafin kudi na shekara ta 2021 da gwamnan ya gabatar ga majalisar dokoki jihar ya nuna cewa bangaren ilimi ba ya cikin abubuwa uku na farko da aka fi ware wa kudi a cikin kasafin.

Kasafin kudin jihar na 2021 ya nuna cewa an ware wa ilimi kudi Naira biliyan 3.69, abin da ke nuna cewa yana kasa da bangaren samar da muhalli wanda aka ware wa Naira bikiyan 8, da bangaren ayyuka wanda aka ware wa Naira biliyan 7.84, haka nan ma an ware Naira biliyan 4.52 ga bangaren kasuwanci da masana'antu da yawon shakatawa.

A lokacin da aka yi masa tambaya game da rashin zaman sa a jihar Yobe sanadiyyar rikon da yake yi na mukamin shugaban jam'iyyar APC na kasa, gwamna Mala Buni ya ce aikinsa na shugabancin APC ba ya yin cikasa ga kokarinsa na sauke nauyin aikinsa na gwamna.

A wani kaulin gwamnan ya ce yakan yi sama da kwana 3 a cikin jihar a kowane wata, daga baya kuma ya ce a kusan kowaqne mako ma yakan kwashe kimanin kwana 3 a jihar.

Sannan ya tabbatar da cewa yakan gudanar da ayyukansa yadda ya kamata koda ba ya Damaturu babban birnin jihar.

Latsa nan domin kallon cikakken shirin