Rikicin Tigray: Abiy Ahmed ya bai wa masu fafutuka sa'a 72 su miƙa wuya

Rikicin ya yi sanadin rasa rayukan daruruwan fararen hula tare da raba dubbai da muhallansu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Rikicin ya yi sanadin rasa rayukan daruruwan fararen hula tare da raba dubbai da muhallansu
An wallafa

Firaministan Habasha ya bai wa dakarun yankin arewacin Tigray wa'adin sa'a 72 su miƙa wuya yayin da dakarun gwamnati ke ci gaba da danna kai cikin birnin Mekelle.

Abiy Ahmed, ya shaida wa shugabannin Tigray cewa "an shiga yanayin da babu zancen juya baya".

Masu fafutuka na ƙungiyar TPLF, da ke iko a Tigray sun lashi takobin ci gaba da yaƙi.

Rahotanni sun ce yaƙi ya yi sanadin rayukan ɗaruruwa da tilasta wa dubbai tserewa a makonnin baya-bayan nan.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan faɗa wa cikin bala'in buƙatar jin-ƙai.

Kafin wannan lokacin dakarun ƙasar sun yi gargadi cewa za su yi wa garin Mekelle mai al'umma aƙalla dubu 500,00 ƙawanya, sannan su kai masa hare-haren makaman atilary.

"Ba za mu ji ƙan kowa ba," a cewar kakakinsu.

Shugaban masu fafutika na TPLF Debrestsion Gebremichael, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa dakarunsa sun yi ƙoƙari wajen datse ko murkushe hare-haren sojojin gwamnati.

"Suna ta kai mana hare-hare akai - akai amma duk a banza," ya shaida wa Reuters.

1px transparent line

Me gwamnati ke shirya wa?

Gwamnati ta ce dakarunta sun ƙwace ikon wasu manyan garuruwa a makon da ya gabata. Sai dai, tabbatar da hakan akwai wahala kasancewar an katse layukan waya da intanet tun soma wannan rikici a yankin.

A wata sanarwa ta ranar Lahadi zuwa ga shugabannin TPLF, Mr Abiy ya ce: "Muna gab da kawo ƙarshen tafiyarku, don haka muna umarta ku da ku miƙa wuya a cikin sa'a 72, saboda tura ta kai bango. Wannan ita ce damarku ta ƙarshe."

Mr Abiy ya ce dakarun TPLF "su miƙa wuya cikin lumana" kuma al'ummar Mekelle su yi mubaya'a ga dakarun gwamnati "domin tabbatar da cewa ƙungiyar ta fuskancin shari'a".

A ranar Juma'a, Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka Ta Kudu, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar haɗin-kan Afirka, ya sanar da naɗa tsoffin shugabannin Afirka uku domin jagorancin tattaunawar sulhu.

Sai dai Ethiopia ta yi watsi da wannan yunƙuri tana mai cewa wannan rikici ne na cikin gida, don haka za ta yi amfani da ƙarfinta wajen kawo ƙarshensa.

"Ba za mu yi sulhu da masu aikata muggan laifuka ba... Za mu hukunta su, ba wai jiran hawa teburin sulhu ba," a cewar Mamo Mihretu, ɗaya daga cikin masu taimaka wa Mr Abiy, kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Abokai da ƴan uwa na Afirka za su taka muhimmiyar rawa idan suka matsawa TPLF mika wuya, kuma saboda wannan babu mutumin da zai je Tigray ko Mekelle domin sanar ko bayyana musu hakan."

Mr Mamo ya ce tsoffin shugabannin daga Mozambique da Liberia da Afirka Ta kudu - da ke shirin zuwa ƙasar nan da yan kwanaki - ba za su samu damar isa Tigray ba saboda farmakin sojoji da ake kai wa.

An katse layukan sadarwa da sufuri tun soma yaƙin.

Mr Mamo ya ce gwamnati na yin duk mai "yiwuwa" domin bai wa Majalisar Ɗinkin Duniya damar kai wa mazauna yankin Tigray taimakon gaggawa.

1px transparent line

Me ya haddasa wannan rikici?

Wannan rikici ya samo asali ne daga tsarin gudanar da gwamnatin ƙasar Ethiopia.

Tun a 1994, Ethiopia na amfani da tsari irin na gwamnatin tarayya wanda hakan ya sa ƙabilu da dama ke lura da gudanarwar yankuna 10 na ƙasar.

Idan aka tuna, jam'iyya mai ƙarfi ta yankin Tigray - Tigray People's Liberation Front (TPLF) - ta taka muhimmiyar rawa wurin samar da wannan tsari.

Jam'iyyu huɗu ne suka yi haɗaka suka samar da shugaban da ya mulki ƙasar tun daga 1991, bayan an yi wa sojoji juyin mulki.

A ranar 4 ga watan Nuwamba Firaminista Abiy Ahmed ya umarci dakarun gwamnati su kai hari kan dakarun Tigray bayan ya ambata cewa an kai wa sansanonin soji hari.

An samu rikici sosai da hare-haren sama tun daga lokacin.

Ƙungiyar TPLF ta kasance mafi karfin mambobi a gamayyar jam'iyyun da ke mulkin Habasha a tsawon shekaru, sai dai Mr Abiy ya daƙile tasirinta bayan hawa mulki a 2018 kuma TPLF ta bijirewa shiga jam'iyyar da aka haɗe wuri guda.

Shugabannin Tigray sun ce ana musu rashin adalci da zarge-zagen rashawa.

Mr Abiy ya zargi wasu daga cikin shugabanin Tigray da "rashin adalci" da adawa da shirinsa na sake fasalta Habasha.

Map

Munin rikicin

Rahotanni na cewa gwamman mayakan Tigrai sun rasa rayukansu, kuma wasunsu sun jikkata, har an kai wasunsu zuwa asibitoci a yankin Amhara mai maƙwabtaka da yankin na Tigray.

MDD ta ce wannan yakin na iya tilasta wa mutum miliyan tara barin muhallansu da garuruwansu -- kuma akwai kayayyakin jin ƙai da ba za su kai ga al'umomin da ke bukatarsu ba.

Ƙungiyoyi na ƙorafin cewa ba sa iya kutsawa domin kai taimako ga farar hula da suka maƙale, sannan akwai fargabar dubbai sun mutu.

bb

Yakin na Tigray ɗaya ne cikin jerin matsalolin da ke addabar Habasha, wadda rikicin ƙabilanci yake son kara raba kawunan ƴan ƙasar.

Kafin wannan lokacin Habasha ta kasance ƙasar da ke taimakawa wajen wanzar da zaman lafiya a yankin kusuwar gabashin Afirka, amma yanzu ita ce ke kan gaba wajen ruruta wutar rikici da ka iya raba yankin da zaman lafiya.