Diabetes: Yau ce ranar yaƙi da ciwon, ya alamominsa suke?

An wallafa

Majalisar Ɗinkin Duniya ta keɓe kowacce ranar 14 ga watan Nuwamba don gangami da fadakar da jama'a a kan ciwon suga.

Taken na bana ya yi duba ne a kan irin gudunmuwar da ma'aikatan jinya kan bayar ga masu fama da wannan cuta.

A duniya baki daya an yi hasashen cewa akwai mutum fiye da miliyan 560 d ake fama da wannan cuta.

Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa, likita ne da ya ƙware a fannin kula da masu irin wannan cuta, ya shaida wa BBC cewa, abin da ke haifar da wannan cuta shi ne kasawa ko rashin wani sinadari da ke cikin jikin mutum wanda ake kira 'Insulin' a turanci, hakan na faruwa ne ko a dalilin wata jinya da ke jikin mutum.

Likitan ya ce, irin wannan rashin sinadari na insulin ɗin a jikin mutum shi ake kira nau'i na farko na wannan cuta ta suga.

Daktan ya ce,"Akwai nau'i na biyu na wannan cuta wanda ake kira type 2, ita a wannan yanayi mutum zai kasnace yana da sinadarin insulin din amma baya aiki sosai".

Ya ce an fi samun yara daga shekara 20 zuwa ƙasa da ke kamuwa da nau'i na farko na ciwon suga wato type 1, nau'i na biyu kuwa daga shekara 20 zuwa sama take kamawa.

Wadanne alamomi ne mutum zai gane cewa ya kamu da ciwon suga?

Dakta Salihu Kwaifa, ya ce an fi ganin alamomin ciwon suga ga wadanda suka kamu da ciwon nau'in farko wato type 1, shi ne inda za a ga mutu na rama da yawan fitsari da yawan shan ruwa dama yawan jin kishirwa.

Liktan ya ce,"Ga wadanda suka kamu da ciwon nau'i na biyu ba sa jin komai, sai a wasu lokuta mutum zai rinƙa laulayi kamar rashin lafiya, a wani lokaci mutum zai iya ramar ko yawan fitsarin, amma an fi gane mutum na da ciwon idan ya na wata rashin lafiyar yaje asibiti aka yi masa gwajin jini sai aga ciwon".

Ta wacce hanya ake kamuwa da wannan cuta?

Likitan ya ce, ita cutar nau'i ta ɗaya tafi alaka da jini ma'ana gadonta ake, idan iyayen mutum na da ita ko wani ɗan uwansa sai mutum ya ga ya kamu da cutar.

Dakta Ibrahim a wasu lokutan ba sai mutum ya gada ba, kiba na haddasa ciwon, sannan rashin motsa jiki ma na janyo haka da kuma cin abinci mai suga kamar Carbohydrates a turance sannan ba a motsa jiki.

Likitan ya ce ba cin abincin ne mai illa ba, aci ba a motsa jiki ba shi ke haddasa wannan cuta ta siga.

Karin Labaran da zaku so karantawa?