Zaben Ivory Coast: Alassane Ouattara ya yi tazarce a zaben da ƴan adawa suka ƙaurace

An wallafa

Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya yi tazarce wa'adi na uku a zaɓen shugaban ƙasa mai cike da ƙalubale wanda ƴan adawa suka ƙaurace.

Hukumar zaɓe a Ivory Coast ta ce Shugaba Alassane Ouattara ya sake lashe zabe a karo na uku, bayan samun kusan kashi casa'in da huɗu cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zaben na ranar Asabar.

Shugaban ya samu kashi 94 na yawan ƙuri'un da aka ƙada, kuma a wasu wuraren da yake da dimbin magoya baya ya lashe kashi 99 na kuri'u

Zaben wanda aka bayyana cewa kashi 54 na masu ƙada Kuri'a ce suka fito, dole ne sai Majalisar Tsarin Mulki ta tabbatar da sakamakon zaɓen

A ranar Litinin, 'yan adawar ta Ivory Coast sun ce za su kirkirar gwamnatin rikon kwarya da za ta gudanar da wani sabon zaɓen

Manyan ƴan adawa Pascal Affi N'Guessan da kuma Henri Konan Bédié sun buƙaci magoya bayansu su ƙauracewa zaben.

Dukkaninsu ba wanda ya samu kashi uku na kuri'un da aka kaɗa, kamar yadda alkalumman sakamakon zaben suka nuna.

Mista Ouattara ya sanar da tsayawa takara ne bayan mutuwar wanda jam'iyyarsa ta tsayar don ya gaje shi a watan Yuli.

'Yan adawar sun kira matakin da ya ɗauka a matsayin juyin mulki.

An kashe mutane talatin yayin yakin neman zabe da kuma ranar zabe.

Me ya faru ranar zaɓe

Rikici ne ya mamaye zaɓen kuma masu sa ido sun ce an samu matsaloli yayin gudanar da zaben na Ivory Coast.

Ƙungiyar PTI Advocacy ta ce yawancin al'ummar ƙasar sun yi zaɓen ne cikin tashin hankali.

Ta ƙara da cewa mutane da dama ƴan kasar ne aka hana wa yin zaɓen saboda ba a buɗe rumfunan zaɓen ba.

Kungiyar ta kuma waɗanda suka yi zaben sun yi ne cikin tsoro da fargaba.

Kungiyar ta ƙara da cewa ba a yi zaben ba kusan kashi 23 na rumfunan zaben saboda barazanar hare-hare.

Kungiyar ta kuma ce an tarwatsa runfuman zabe da dama a yankunan da ƴan adawa da ke magoya baya a ranar zaben.

Me hukumomi suka ce

Hukumar zaɓen ƙasar ta bayyana hargitsin da aka samu a matsayin abin da ta kira wani ɗan rikici, wanda bai shafi rumfunan zaɓe ba da dama.

Jami'an tsaro 35,000 aka girke a sassan ƙasar domin kai kayan zaɓen da tabbatar da zaman lafiya kamar yadda ministan tsaron ƙasar ya bayyana.

Bayan ƙada ƙuri'arsa a Abidjan ranar Asabar, Mista Ouattara ya yi kiran kawo karshen zanga-zanga.

"Su daina saboda Ivory Coast na buƙatar zaman lafiya, wannan aikata laifuka muna fatan za su daina, domin bayan zaben kasar ta ci gaba da ayyukanta na ci ba," in ji shugaban