Bidiyon ƴan matan da ke kaɗa jita don samun sauƙin bala'in yaƙi a Afghanistan

Bayanan bidiyo, Bidiyon ƴan matan da ke kaɗa jita don samun sauƙin bala'in yaƙi a Afghanistan
An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ga ƴan matan Afghanistan da dama, suna ganin babu tabbas kan abin da zai faru a nan gaba.

Da yawansu sun afka cikin ruɗani tun suna ƙanana. Sai dai a yanzu an samu wasunsu suna nishaɗantar da kansu da kaɗa jita da waƙe-waƙe.

Ƴan matan waɗanda a da suke saide-saidensu a kan tituna, a yanzu sun yi wata waƙa mai taken Sweet Dreams inda har aka haska wasu mawaƙa na duniya a ciki.

Sunan ƙungiyar waɗannan yara makaɗa dai 'The Miraculous Love Kids,' kuma a birnin Kabul take.

Wakilin BBC Kawoon Khamoosh ya yi ta bin labarin rayuwarsu tun 2016 a lokacin da suka fara koyon kaɗa jitar.