Zaben Amurka na 2020: Ƴan Najeriya 9 da ke takara a zaɓen Amurka

Nigerian-American women dey contest for US general elections

Asalin hoton, April Ademiluyi, Esther Agbaje, Ngozi Akubuike

An wallafa

Baya ga zaɓen shugaban ƙasa a Amurka da za a gudanar ranar Talata, akwai kuma zaɓen wasu gwamnonin jihohi da na kujerun ƴan majalisar wakilai da majalisar dattijai.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya ce ƴan asalin Najeriya tara ne ke takara a zaɓen na Amurka da ke neman lashe kujeru a matakin tarayya da jiha da kuma ƙananan hukumomi

Yawancinsu kuma suna takara ne ƙarƙashin tutar jam'iyyar Democrats da ke adawa da jam'iyyar Republican ta Shugaba Trump.

Oye Owolewa ɗan asalin jihar Kwara

Ƴan Najeriyar sun haɗa da Oye Owolewa ɗan asalin jihar Kwara wanda ke takarar kujerar majalisar wakilai ƙarƙashin jam'iyyar Democrats.

Mista Owolewa mai shekara 30, da ke takarar domin wakiltar gundumar Columbia a Washington DC zai kasance ɗan Najeriya na farko a majalisar wakilan Amurka.

Yomi Faparusi ɗan asalin jihar Ekiti

Mista Yomi Faparusi ɗan asalin jihar Ekiti, yana takarar kujerar majalisar dattijai domin wakilar jihar Tennessee a Amurka.

Mista Faparusi wanda ke da digirin digirgir a jami'ar Ibadan a ɓangaren likitanci da kuma gidiri na uku a Jami'ar Hopkins ya taɓa fitowa takarar ɗan majalisar wakilai a 2014 da 2016 amma duka yana shan kaye.

Yinka Faleti ɗan asalin jihar Lagos

A Missouri, jihar da Republican ke mulki, Yinka Faleti daga Lagos yana takarar ofishin sakataren harakokin waje.

Bayanai sun ce mista Faleti tsohon sojan Amurka ne tsakanin 1998 zuwa 2004.

Paul Akinjo ɗan asalin jihar Ondo

Paul Akinjo ɗan asalin jihar Ondo yana takarar neman kujerar ɗan majalisar jiha ƙarkashin jam'iyyar Democrat.

Mista Akinjo ya taba zama mataimakin magajin garin Lathrop, a California.

Adewunmi Kuforiji ɗan asalin jihar Oyo

Adewunmi Kuforiji ɗan asalin jihar Oyo yana takarar kujerar majalisar wakilai a Delaware. Ya lashe zaɓen fidda gwani a 15 ga Satumba inda ya doke abokin takararsa Robert Haynes.

Zai fafata ne da mai rike da kujerar Lyndon Yearick, wanda ya kada shi a zaɓen rabin wa'adi a 2018.

Esther Agbaje

Esther Agbaje

Asalin hoton, Esther Agbaje

A matakin Jiha Esther Agbaje tana neman kujerar ƴar majalisa a Minnesota ƙarkashin jam'iyyar DFLP wani resh na jam'iyyar Democrats.

Ms Agbaje wacce ta karanci ilimin shari'a a Jami'ar Harvard da kuma digiri na biyu a Jami'ar Pennsylvania, ta yi aiki a ofishin harakokin wajen Amurka.

Ademiluyi da Ngozi Akubuike da Benjamin Osemenam

A matakin ƙanana hukumomi akwai April Ademiluyi da Ngozi Akubuike da Benjamin Osemenam dukkaninsu ƴan Najeriya da ke takara a zaɓen na Amurka