Zaɓen 2020: Biden da Trump na zaryar ƙarshe kafin zaɓen Talata

Asalin hoton, Getty/EPA
Donald Trump da Joe Biden na karaɗe jihohin Amurka a daidai lokacin da zaɓen Amurka ya kawo jiki.
Shugaba Trump ya ziyarci jihohi biyar da ake sa ran za a fafata tsakaninsa da Joe Biden, inda shi kuma abokin hamayyar tasa ya tafi jihar Pennsylvania.
Dan jam'iyyar Democrat Mista Biden ne ke kan gaba a sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka yi gabanin zaben na ranar Talata.
Fiye da mutum miliyan 90 tuni sun yi zabe, matakin da ake sa ran zai kafa tarihi ta bangaren yawan masu kada kuri'a cikin shekara 100.
Trump ya ziyarci jihohi biyar a yunkurinsa na karshe
Dan takarar jam'iyyar Republican din bai huta ba ranar Lahadi, inda ya halarci gangamin da magoya bayansa suka shirya a jihohin Iowa da Michigan da North Carolina da Georgia da kuma Florida.
Yayin wani jawabi da yayi a Washington, wani karamin gari da ke jihar Michigan, Mista Trump ya ce "tattalin arzikin Amurka na habaka fiye da yadda aka taba samu a tarihi."

Asalin hoton, EPA
Biden kuwa na yakin neman zabe a Pennsylvania

Asalin hoton, Reuters
Dan takarar jam'iyyar Democrat kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden ya nufi Pennsylvania ne, jihar da aka haife shi kuma jiha mai muhimmanci a zaben na bana.
Mista Trump ne ya lashe zaben a 2016 amma a bana Mista Biden ne ke kan gaba.
A Philadelphia, Mista Biden ya yi wa Amurkawa bakaken fata a jihar alkawarin duba matsalar nuna bambancin launin fata da ta addabi Amurkawa.
Ya kuma soki yadda Mista Trump ke tafiyar da yaki da annobar korona a kasar:
"Kana iya cewa yana aikata babban laifi ne idan ka dubi yadda yake wa batun rikon sakainar kashi.
'Dubun dubatan mutane sun rasa rayukansu musamman bakaken fata, kuma abu ne da a na iya kauce wa aukuwarsa da ya dauki matakan da suka dace."













