Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mutum 60 ne suka mutu zuwa yanzu a girgizar ƙasa a Turkiyya
Tawagar ceto a yankin Izmir na Turkiyya na ci gaba da neman waɗanda suka tsira daga girgizar ƙasar da aka yi ranar Juma'a, yayin da mahukunta suka tabbatar da mutuwar mutum aƙalla 60 zuwa yanzu.
Jami'ai sun ce mutum 58 ne suka mutu a Turkiyya, yayin da matasa biyu suka mutu a tsibirin Samos da ke cikin ƙasar Girka mai maƙwabtaka.
Har yanzu akwai gwamman mutanen da suka ɓata biyo bayan girgizar ƙasar.
An ceto wani dattijo mai shekara 70 daga ɓaraguzan gini a Izmir bayan ya maƙale tsawon sa'a 33.
Cibiyar US Geological Survey (USGS) ta ce girgizar ƙasar ta kai girman 7.0, amma Turkiyya ta ce 6.6 ce.
Bayanan baya-bayan nan
Ma'aikatan ceto na duba ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe a yammacin Turkiyya a kwana na uku a jere ranar Lahadi, suna masu fatan sake samun waɗanda suke da rai.
Wani mai shekara 70 da aka bayyana sunansa Ahmet Citim, an janyo shi daga ƙarƙashin ɓaraguzai a yankin Izmir da asubahin Lahadi kuma aka kai shi asibiti.
Ministan Lafiya na Turkiyya Fahrettin Koca ya ziyarci Ahmet Citim a asibiti.
A gefe guda kuma, Shugaban Ƙasa Recep Tayyip Erdogan ya sanar da adadin 'yan Turkiyya da suka mutu zuwa 58.
Kazalika, ya ce mutum 896 ne suka jikkata a girgizar ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce baki ɗayan mace-macen sun faru ne a Izmir.