Trump da Biden sun caccaki juna a muhawarar karshe

An wallafa

Donald Trump da Joe Biden sun kalubalanci juna kan ayyukan da suka yi a mahawarar ƙarshe da suka tafka kafin zaben shugaban ƙasa da ke tafe a watan gobe.

Mutanen biyu dai ba su ragawa juna ba wajen kakkausar suka, inda ɗan takararar jam'iyyar Democrats ya ce bai kamata shugaba Trump ya ci gaba da zama a mulki ba bayan Amurkawa dubu dari biyu da ashirin sun mutu sakamakon annobar korona.

A martaninsa cikin hikima da nutsuwa sama da mahawarar farko, Mr Trump ya ce, tsarinsa a kan korona ya ceto rayuka, sannan tsare-tsarensa masu tsauri a gida da waje sun samar da karin ayyuka a Amurka.

Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden ya kuma ce akwai cibiyar nuna kyamar launin fata a Amurka, kuma Donald Trump na daya daga cikin shugabanni mafi nuna wariya a tarihi.

A martaninsa Shugaba Trump ya ce, babu wani shugaba da ya taba yiwa al'ummar bakar-fata irin hidimar da ya yi musu, kuma a dakin da suke shi ne wanda yafi kowa sassauci wajen nuna wariya.

Mista Trump ya kare matsayin gwamnatinsa kan muhalli. Ya na mai cewa ya janye Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris saboda ya fahimci babu adalci a ciki kuma dubban Amurkawa zasu rasa ayyukansu.

Joe Biden ya ce dumamar yanayi barazana ce da tun yanzu ana ganin tasirinta, don haka nashi tsare-tsaren kan sauyin yanayi zasu samar da ingantattun ayyuka.

Haka dai ƴan takarar suka yi ta sukar juna a bangarori daban-daban a yayin muhawarar.