EndSARS: Yemi Osinbajo ya magantu kan harbin masu zanga-zanga

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Yemi Osinbajo, ya yi magana kan harbe-harben da aka yi kan dubban masu zanga-zangar EndSARS a babban titin Lekki da ke birnin Legas.

"Zuciyata na tare da mutanen da harbe-harben Lekki ya shafa, da 'ƴan sanda da sauran mata da maza da suka rasa rayukansu a cikin ɗan tsukukun nan a yankuna daban-daban na Legas da sauran jihohi." Inji Osinbajo.

Shi ne sakon da mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya wallafa a shafinsa na Twitter don kwantar da hankulan 'ƴan Najeriya bayan buɗe wuta da jami'an tsaro suka yi wa masu zanga-zanga a Lekki, inda mutum 12 suka mutu a cewar rahotan ƙungiyar Amnesty.

Wannan shi ne karo na farko da wani mutum daga fadar shugaban ƙasar ke magana a kan kisan, bayan shafe sama da sa'a 24 da sojoji suka bude wuta kan masu zanga-zangar lumana.

"Muna addu'ar kar wannan yanayi ya sake maimaita kan sa...." a cewar Mataimakin shugaban kasar.

Tun bayan faruwar wannan al'amari mutane a ciki da wajen ƙasar suka harzuka da yin kira ga gwamnati ta kawo ƙarshen kashe matasan da ke zanga-zangar lumana.

Wanann yanayi da Najeriya ta tsinci kanta ya ja hankalin ƙasashen duniya da alla-wadai daga sassa daban-daban da kuma fitattun mutane.

Ƙungiyar Ecowas ta gargadi jami'an tsaron Najeriya kan amfani da ƙarfi sama da kima kan masu zanga-zanga. Sojojin Najeriya dai sun musanta zargin da ake musu kan buɗe wa matasan wuta.

Har yanzu dai hankula na tashe kuma ana ci gaba da samun tarzoma duk da dokar hana fita ta sa'a 24 da gwamnati ta sanya a Legas domin lafar da kurar rikici da ke neman kassara jahar.