Ranar Lafiyar Ƙwaƙwalwa Ta Duniya 2020: Yadda za ku guje wa damuwa don gudun ''taɓin hankali''

An wallafa

Kana fama da wata damuwa da ta kai ka maƙura har ka ji ba za ka iya jurewa ba? Kar ka bar abin kai kaɗai ya dame ka. Ga wasu hanyoyin da za su taimaka.

Kana fama da wata damuwa? Ta kai ka maƙura? Ta ƙure ƙarfinka? Ba ka da wata dabara?

Kana ji kamar aikin da kake yi ya yi maka yawa, duk da cewa a baya aikin bai taɓa jefa ka cikin wannan yanayi ko ya dame ka ba?

Watakila rayuwar cikin gida na tattare da ayyuka da kai komo da bai ƙarewa, da har ya kai ga ba ka ganin akwai mafita?

To, wadannan dai alamomin ne da ke nuna ka doshi ko tsintar kai cikin yanayi na taɓin hankali.

Amma dai kada ka tsorata, ƴar jarida kuma likita Radha Modgil na da wasu hanyoyin da za su taimaka wajen dawo da kai daidai, da kuma shawarwari ta yada za ka gane idan taɓin hankali na neman shafar ka, sai ka kimtsa masa da kare kai kafin a kai matsayin da komai zai dagule.

Me ake nufi da taɓin hankalin damuwa?

Fitaccen masanin halayyar dan adam Herbert Freudenberger ne ya soma amfani da kalmar "taɓin hankalin damuwa" a wani bincike da ya wallafa a 1974.

Ya bayyana shi a matsayin "wani yanayi na gajiyar ƙwaƙwalwa" da yanayin aikin da mutum ke yi ke haifarwa, wanda hawa-hawa ne ciki har da " kokarin tilasta bayanan matsayin kai".

A ƴan kwanakin nan muna tunanin taɓin hankalin da damuwa ke haifarwa, "gajiya mara misaltuwa da babu iyaka" a cewar Dr Radha Modgil, wadda ta ce, na sa mutum ya ji kamar ba zai iya ci gaba ko ya gaji da rayuwa".

Ba kamar Herbet Freudenberger ba, Dr Modgil na da yardar cewa irin wannan damuwa na faruwa ta hanyoyi daban-daban ba sai a wurin aiki kaɗai ba.

Ya ake ji?

Dr Modgil ta kwatanta taɓin hankalin da damuwa ke haifarwa da salon yadda batirin waya ke ƙarewa.

"Haka kake jin ka gaji da rayuwa, kamar babu sauran ruwan ajiya a cikin tanki," in ji ta.

Watakila kai mutum ne da ka saba jurewa wahalar rayuwa da ƙalubale a wajen aiki amma a wannan lokaci kana ta fama.

Ko da yake, Dr Modgil ta ce wannan alama ce da ke nuna cewa ɗaya daga cikin "rumbunan da ke daukar damuwarka" ya soma raguwa.

"Ka yi nazari kamar haka, kana da rumbun aiki da na gida. Idan ɗaya daga cikinsu ya ragu ɗaya kuma ya ƙaru, to babu shaka za ka iya tsira."

"Amma idan duk suka yi ragu babu komai saura a adane, daga nan matsalar take somawa."

"Batarin da ke daukar damuwarmu na bukatar kulawa, kamar wayar hannu", a cewarta, "akwai bukatar ka tambaye kan ka: 'Ta ya ya zan yi caji?"

Me ke jawo haka?

Dr Modgil ta ce "duk wani babban sauyi a rayuwa ko aukuwa" na ba da gudunmawa wajen damuwa da ke haifar da taɓin hankali.

Ta bayar da misali da matsalolin kuɗi da alaka ta ma'aurata ko soyayya.

Da kuma sauran nau'ikan damuwa, kamar sauya gida, rasa aiki ko faduwa jarrabawa.

Don haka ta yaya za mu daƙile damuwa da ke shafar ƙwaƙwalwa da kare kan mu da ga shiga irin wannan yanayi?

Hanyoyin kare kai daga shiga damuwar haifar da taɓin hankali...

Dr Modgil ta ce:

·Ka/ki kasance mai sauraro zuciyarka da abin da kike so sosai.

·Mayar da hankali kan abin da ke tafiya da kyau a rayuwarki.

·Kasance da abokai da ke sa ki farin ciki.

·Yawaita motsa jiki.

·Yawaita abubuwan da ke sa ki farin ciki ya kasance abin da kike bai wa fifiko.

·Yawaita sauraron wakar da ke saka farin ciki.

·A rinka samun isasshen bacci.

·Kar a kai matakin da lokacin zai ƙure. Wadannan su kasance dabi'a da ka gina kan ka akai kuma su kasance kullum ana yin su.

Dr Radha Modgil na fatan wadannan bayanai na ta za su kare mutum daga damuwa da ke shafar ƙwaƙwalwa.

Tana kuma da yaƙinin cewa idan ka bai wa damuwarka fifiko a kullum, kamar yadda muke yi da batirin waya, za mu ga babban ci gaba a duk matsalolinmu da lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa.

Wannan maƙala ce ta musamman daga BBC.