Yadda makiyaya ke tafka asarar miliyoyin CFA a Kamaru

Bayanan sautiCameroon cattle rustlers
An wallafa

Latsa alamar lasifikan da ke jikin hoton da ke sama domin jin hirar.

Wani bincike da kungiyar ci gaban al'adu da raya tattalin arzikin Fulanin Mbororo makiyaya a Kamaru ta yi, ya gano cewa makiyaya a faɗin lardin Adamawan Kamaru na yin asarar shanu sama da dubu daya duk bayan watanni shida.

Kungiyar mai suna "Mbororo Social and Cultural Development Association" ko kuma MBOSCUDA a takaice, ta ce darajar wannan asarar ta kai kudin CFA sama da miliyan 265.

Wakilin BBC a Kamaru Mohaman Babalala, ya tattauna da tsohon shugaban matasan Mbororo na Adamawan Kamaru, Oumarou Mbororo Iya Hamajangi kan halin rashin tsaron da ya addabi makiyaya a arewacin Kamaru da abin da suke yi domin shawo kan lamarin.