Hular fasto, ambaliyar ruwa: Hotunan Afirka na wannan makon 05/09/2020

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓun hotunan abubuwan da suka faru a nahiyar Afrika a wannan makon:

Tsietsi Makiti (R) the founder and leader of Gabola church gestures while praying during the Sunday sermon at Bunny's Tavern in Evaton on August 30, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi an gudanar da ibada ta ba kasafai ba a wurin sayar da abinci na Bunny's Tavern a Afrika Ta Kudu domin yin murnar matakin gwamnati na amincewa a ci gaba da da sayar da barasa...
Tsietsi Makiti

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ... Tsietsi Makiti ya kafa cocin mai suna Gabola domin jan hankalin mabiya wadanda ba sa zuwa Cocin Pentecostal
Lyon's French forward Moussa Dembele (L) and Dijon's Gabonese defender Bruno Ecuele Manga (R) jump to head the ball during the French L1 footall match between Olympique Lyonnais (OL) and Dijon FC on August 28, 2020, at the Groupama Stadium in Decines-Charpieu, near Lyon, central-eastern France.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Juma'a ɗan wasan Gabon Bruno Ecuele Manga (hanun dama) ya yi karo da ɗan wasan Lyon dan ƙasar Faransa Moussa Dembele lokaci da suke fafatawa da Dijon Fc a Faransa
A Student wears a face mask as she studies on her first day back at Chiekh Anta Diop University in Dakar on September 1, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata ɗalibai sun koma jami'a a Dakar babban birnin Senegal
KhoiSan people wave in solidarity with Bikers United Against Farm Murders and Racism as they ride past the Union Buildings in Pretoria, on August 29, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar Khoisanawa da ke Afrika Ta Kudu suna daga hannu domin nuna goyon baya ga mahaya ababen hawa da ke zanga-zanga kan kashe-kashen da ake yi a gonakin birnin Pretoria da ke Afrika Ta Kudu...
Bikers representing various clubs ride to the Union Building to lay crosses and flowers to symbolize the murdered farmers across the country on August 29, 2020 in Pretoria, South Africa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, ...Mahaya ababen hawan suna buƙatar gwamnati ta ɗauki ƙarin matakai domin hana kashe manoma
Algerian journalists rally to demand the release of their colleague Khaled Drareni in the capital Algiers on August 31, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin 'yan jarida sun yi zanga-zanga inda suka buƙaci a saki abokin aikinsu Khaled Drareni, wanda a farkon wata aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan yari
Sudan's ousted President Omar al-Bashir appears in court in Khartoum, Sudan on September 1, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Talata tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya gurfana a gaban kotu inda aka soma yi masa shari'a a kan rawar da ya taka a juyin mulkiin 1989
A Libyan migrant (R) and an east African migrant pray a Muslim prayer for reconciliation onboard the Sea-Watch 4 civil sea rescue ship on September 01, 2020, on sea off the coast of Sicily, Italy,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Talata wani ɗan gudun hijrar Libya tare da takwaransa na Gabashin Afrika suna addu'a a jirgin da ya ceto su daga Tekun Mediterranean wanda Banksy ya ɗauki nauyi lokacin da suka fahimci cewa an ba su damar shiga Italiya.
A woman with a mask stands as migrants are evacuated by police in front of the town hall of Paris, on September 1, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kazalika ranar Talatar dai 'yan sanda sun kwashe 'yan gudun hijra wadanda galibun su 'yan Somalia da Ivory Coast da Afghanistan ne daga wani ɗakin taro a Paris.
A Sudanese resident sits on flood barriers in the capital Khartoum's southern neighbourhood of al-Kalakla, on August 31, 2020.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Litinin wani mazaunin birnin Khartoum yana kallon ruwan da ya yi ambaliya lamarin da ya yi ajalin a kalla mutum 90.
Justin Walters of South Africa plays a shot on the driving range prior to the Estrella Damm N. A. Andalucia Masters golf tournament at Real Club Valderrama on September 2, 2020 in Cadiz, Spain.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Laraba kuwa ɗan wasan ƙwallon Golf na Afrika Ta Kudu Justin Walters yana gwaji gabanin gasar da zai je a Spnaiya.

Haƙƙin mallakar hotuna AFP da Getty Images da EPA da kuma Reuters.