Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tall Track: Sabuwar waƙar Burna Boy da ke jan hankalin matasa a Najeriya
Sabon album ɗin mawaƙi Burna Boy ya ja hankalin matasa sosai musamman a kafofin sadarwa na intanet bayan sakinsa da safiyar Juma'a.
Waƙar mai suna 'African Giant' album ɗinsa na biyar kenan, wani mawaƙin Amurka Sean Diddy Combs da Bosede Ogulu, furodusan waƙar.
Ga aikin samar da wakokin guda 15 a album din ya kuma ƙunshi wasu mawaka kamar Stormzy, Coldplay's Chris Martin, Youssou N'Dour, Naughty By Nature, da Sauti Sol.
Ina za ka iya saurare?
Inda za a iya saukewa da sauraren wakokin album din sun hada da rumbun wakoki na apple, Boomplay, ITunes, deezer, YouTube, rumbun Google Play da napster, kamar shafin African Giant ya sanar a Tuwita.
Ga jerin waƙoƙin album ɗin
- 'Level Up (Twice As Tall)' [Tare da Youssou N'Dour]
- 'Alarm Clock'
- 'Way Too Big'
- 'Bebo'
- 'Wonderful'
- 'Onyeka' (Baby)
- 'Naughty By Nature' [Tare da Naughty By Nature]
- 'Comma'
- 'No Fit Vex'
- '23'
- 'Time Flies' [Tare da Sauti Sol]
- 'Monsters You Made' [Tare da Chris Martin]
- 'Wetin Dey Sup'
- 'Real Lif[Tare da Stormzy]
- 'Bank On It'
Me ake cewa game da waƙoƙin?
Ga alama dai wannan waƙa ta farantawa mafi yawan masu amfani da shafin tuwita a Najeriya sun aunaci waƙar don kuwa sun yi ta amfani da maudu'in da aka ƙirƙira da sunan sau fiye da 260,000 a ranar Juma'a.
Ga abin da wasu suka ce a Twitter:
Wani mai suna Diddy cewa ya yi ''Wannan shi ne album na shekara! Waƙar #TWICEASTALL ta @BurnaBoy.
Ɗaya daya cikin fitattun mawaƙa a Najeriya da ya taɓa lashe lambar yabo Innocent Idibia da aka fi sani da 2Face ya ce "Wannan ya wuce kyautar Grammy".
@prince_ikpeme ya ce: ''Har an kalli waƙar sau milyan 5.32 a manhajar audio mack. Kuma har ba a gaji da kallo ba!! Gskiya Burna ya zama zakaran gwajin dafi. Wuta dai.''
Mai taimaka wa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan shafukan sada zumunta ba a bar shi a baya ba. Bashir Ahmad ya wallafa cewa: ''Ya sake mamaye harkar, @burnaboy mutumina. #AfricanGiant yanzu kuma #TwiceAsTall
@BlackCoffee ya ce: An gaishe ka Sarki @burnaboy #TWICEASTALL 23 ce wacce na fi so!!!!
Allah Ka yi wa Burna Boy albarka ta shekara 600. #TWICEASTALL ta yi wuta.