Yadda korona ta kassara wasu kamfanonin Najeriya

An wallafa

Ɓullar annobar korona ta zama sanadiyar faɗawar miliyoyin mutane cikin talauci a faɗin duniya. Tun bayan ɓullar wannan cuta a Najeriya, manya da ƙananan masana'antu sun girgiza, inda da dama daga cikinsu suka faɗa cikin wani hali.

Wannan annoba ta tursasa wa kamfanoni da dama korar ma'aikata, wasu 'yan kasuwa kuma suka samu karayar arziƙi sakamakon yadda abubuwa suka tsaya cik a lokacin kullen korona da ma bayan kullen a wasu ɓangarorin.

Duk da cewa babu ƙididdiga ko kuma alƙaluman adadin jama'ar da cutar ta kassara a hukumance a Najeriya, sai dai ana hasashen cewa kamfanoni da dama sun soma durƙushewa.

Za a iya cewa kamfanoni da ma'aikatu masu zaman kansu ne suka fi shan wuya sakamakon sun dogara ne ga abin da suke yi domin samun kuɗin shiga, ba kamar gwamnati ba da ke da hanyoyi masu yawa.

Ko a 'yan kwanakin nan sai da wani katafaren kanti mai sassa daban-daban a ƙasar ya bayyana yiwuwar daina gudanar da harkokin kasuwancinsa a Najeriya.

Malaman makarantu ma na ta kokawa a ƙasar ganin cewa makarantu sun shafe sama da watanni huɗu a kulle kuma babu albashi.

Wasu masana tattalin arziƙin na cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, dubban masana'antu za su durƙushe a ƙasar.

Farashin dala a Najeriya ya tashi zuwa kusan N470 a kan kowace dala ɗaya, wanda hakan ba ƙaramar matsala ce ba ga tattalin arziƙin Najeriya da kuma na kamfanoni masu zaman kansu.

Shoprite na shirin janyewa

Ba abin mamaki ba ne a ce annobar korona ta bayar da gagarumar gudunmuwa wurin yunƙurin tasa ƙeyar Shoprite daga Najeriya duk da cewa kamfanin wanda asali na 'yan Afrika Ta Kudu ne ya ce ya samu raguwar kashi 5.9 cikin 100 na kasuwarsa a kasar a 2019 da kuma kashi 6.4 daga watan Janairu zuwa Yuni na 2020 saboda annobar korona.

Shoprite ya buɗe kanti a Najeriya ne a 2005, wanda ya bayyana a matsayin inda yake "sayar da dukkan, ko akasarin kayansa."

Sai dai kamfanin ya fuskanci ƙalubale daban-daban a shekarar bara sakamakon karan tsana da wasu 'yan ƙasar suka ɗora masa wanda har ya yi sanadiyar wasu matasa a ƙasar suka lalata wasu daga cikin kantuna na Shoprite ɗin a Najeriya.

Matasan sun yi hakan ne a matsayin ramuwar gayya kan cin zarafi da kuma nuna wariya ko kuma tsanar da ake zargin ana yi wa 'yan Najeriya a Afrika Ta Kudu, ƙasar da kamfanin ya fito.

Wannan dambarwa dai ta jawo shagunan Shoprite din su rufe na ɗan wani lokaci a faɗin ƙasar, kuma hakan ya jawo mu su asara.

Kamfanin jirgin Air Peace ya kori ma'aikata 70

A cikin wannan makon ne kamfanin jirgin sama na Air Peace ya bayyana korar ma'aikatansa 70.

Kamfanin jirgin ya ce zabi biyu ne kawai da shi: ko dai ya kori wasu ma'aikatan kuma ya rage wa wasu albashi, ko kuma ya yi durkushewar da ba zai iya biyan albashin ba da kuma wasu ayyuka, wanda hakan ya sa ya zaɓi na farko.

Irin wannan yunƙurin da kamfanin jirigin ya yi na korar ma'aikata na daga cikin illolin da annobar korona ta yi wa ma'aikatu da kuma ma'aikata.

A makonnin baya, shugaban kamfanin Air Peace Allen Onyema, ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta samar da wasu kudaden tallafi ga kamfanonin jiragen domin su ci gaba da tsayawa kan kafafunsu.

Kamfanin jirgi na Bristow Helicopters ya kori ma'aikata 100

Shi ma Bristow Helicopters wanda kamfanin akasarin jirgi mai saukar ungulu ne a Najeriya, ya kori matuƙa jirgi da kuma injiniyoyi 100 a ci gaba da faɗi-tashin da ɓangaren sufurin yake yi sakamakon annobar korona.

Wannan korar da kamfanin Bristow ya yi na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan kamfanin jirgin sama na Air Peace ya kori ma'aikata 70 a ƙasar.

Kamfanin Bristow Helicopters ya fuskanci matsi sakamakon annobar ta korona kuma ya ce matakin ba mai sauƙi ba ne, wanda ya zama dole ya ɗauka yayin da yake ta ƙoƙarin yin garambawul ga ayyukansa.

Kamfanonin sufurin jiragen helikwafta na samun kwastomomi ne akasari ta hanyar aiki da ɓangaren man fetur da iskar gas a Najeriya.