Yadda mazauna Abuja ke ji game da janyewar kantin Shoprite

Bayanan bidiyo, Yadda mazauna Abuja ke ji game da rufe kantin Shoprite
An wallafa

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu game da hukuncin kantin sayar da kayayyaki na Shoprite yake shirin ɗauka na janyewa daga Najeriya.

Tun da safiyar Litinin ne kamfanin ya ce yana duba yiwuwar rufe shagunan nasa saboda faɗuwar da ya samu ta kashi 5.9 cikin 100 a 2019 da kuma kashi 6.4 daga watan Janairu zuwa Yuni na 2020 saboda annobar korona.

Tuni wasu suka riƙa bayyana ra'ayoyin nasu a shafukan zumunta.

Wannan cewa yake yi: "'Yan mata ku sha kuruminku, Shoprite ne zai bar Najeriya ba ginin Shoperite ɗin ba, saboda za ku ci gaba da ɗukar hotunanku."

Shi ma wannan cewa ya yi: "Jama'a lokaci ya yi na komawa WhatApp mu duba ƙananan Shoperite da muke da su."