'Yadda na gaji ɗorin gargajiya daga wajen mahaifina'

Bayanan sautiYadda na gaji dorin gargajiya a wajen mahaifina
An wallafa

Latsa hoton da ke sama don sauraron tattaunawa da mace mai dorin gargajiya

Ba kasafai ake jin mace na yi wa maza gyaran targade ko karaya ba a kasar Hausa saboda yanayin al'ada da addini.

Sai dai akan samu kalilan wadanda 'yan gado ne.

Aisha Shariff Baffa ta je Sabon Garin Maɗora da ke birnin Dutse na Jihar Jigawa, inda ta tattauna da wata matashiya wadda ke yi wa kowa da kowa gyara.

Ta kuma fara ne da bayanin sunanta da kuma tsawon shekarun da ta shafe tana ɗorin gargajiya.