Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sam Smith da Burna Boy: Abubuwan da suka kamata ku sani kan wakar 'My Oasis'
Fitaccen mawakin nan na Ingila Sam Smith ya sanar cewa ranar Alhamis din nan zai fitar da wakarsa mai suna 'My Oasis' wadda ya yi tare da mawakin Najeriya Burna Boy.
Shi kuwa Burna Boy, wannan hadin gwiwar na zuwa ne bayan wakar Jerusalema wadda ya yi da Master KG a watan Yuni.
Smith ya wallafa bidiyon kayan kidan da ya yi wakar tare da mawakin na Najeriya a shafinsa na Instagram.
Wannan ce waka ta farko da zai fitar tun watan Afrilu bayan wakarsa da Demi Lovato mai suna 'I'm Ready'.
Sam Smith ya yi wakoki da dama cikinsu har da 'Money On My Mind', 'Stay with Me' da kuma 'Writing's On the Wall', wacce ta sanya ya lashe gasar Oscar in 2016.
Ana hasashen cewa mawakin na Birtaniya ya mallaki £33m.
Yadda masu son wakoki suka ji da hadin gwiwa tsakanin Sam Smith da Burna Boy
Magoya baya sun yi ta yaba wa Burna Boy bisa hada gwiwa da ya yi da Sam Smith. Koda yake har yanzu wakar ba ta fita ba, amma tuni suka fara cewa za ta yi dadi.
Mawakin na Birtaniya ya wallafa sakon Twitter da ke cewa "ina matukar kaunar Burna. Za mu kayatar da kowa".
A martanin da ya yi, Burna ya ce "za mu burge magoya ba ni da kai, Sam."
Wani mai son wakokin Burna, mai suna The Boogie Man, ya yaba kan yadda ake damawa da gwanin nasa yana mai cewa kowanne mawaki yana son hada gwaiwa da shi.
Ba wannan ne karon farko da Burna ya hada gwiwa da mawakan Turai da Amurka ba, domin kuwa a baya ya yi waka tare da Beyonce, Stormzy da kuma Ed sheeran.