'Yan majalisar Kano na son a riƙa fiɗiye masu fyade a jihar

An wallafa

Majalisar dokokin jihar Kano ta fara duba yiwuwar sauya dokokin hukunta masu fyade a jihar domin tsaurara su, ta yadda idan zai yiwu a riƙa fiɗiye masu irin wannan laifi.

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Hon. Nuradeen Alhassan ne ya gabatar da kudurin, inda ya nemi abokan aikinsa su amince da hukuncin 'fidiya' a kan duk wanda kotu ta samu da laifin a nan gaba.

Ya shaida wa BBC cewa tun da dokar da ake da ita a yanzu ba ta sauya komai ba, lokaci ya yi da za a sauya ta, duba da yadda al'ummar Kano suka nuna bukatar hakan.

''Mutane gani suke kamar abin wasa ne, domin idan ana zargin mutum da fyade sai ka ga kafin ma a kai shi kotu, zai dauko lauyansa, karshe ma abin ya zama shiririta'' In ji shi.

Bisa dokokin da ake da su a yanzu a jihar Kano, idan kotu ta kama mutum da aikata fyade zai iya fuskantar daurin shekara goma sha hudu a gidan yari.

Sai dai yan majalisar na cewa wannan bai wadatar ba, mai yiwuwa ma shi yasa ake samun karuwar matsalar har kawo wannan lokaci.

A baya-bayan nan dai hankulan al'ummar Najeriya sun yi matuƙar tashi sakamakon ƙaruwar ayyukan fyaɗen da ake samu.

Fyade bai tsaya a kan manya ba ko 'yan mata ba, galibi a wannan zamanin an fi cin zarafin kananan yara da jarirai.

Rundunar yan sandan jihar kano ta ce sama da kashi 40 na waɗanda ake yi wa fyaɗe, bayan an yaudare su da kuɗi ko abinci ne ake aikata laifin.

Shi yasa take shawartar jama'a da a ko da yaushe yaushe ana shawartar mazauna unguwanni da suka ƙara sanya ido a kan take-take da kai-komon mutane a yankunan, da nufin kare 'ya'yansu da kuma iyalansu.

Yadda matsalar ke karuwa.

A baya bayan nan Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wani mutumi bisa zargin yi wa mata 40 fyade a jihar.

Daga bisani ne kuma ta sake cafke wani mutumi da shi kuma ake zargin ya yiwa wata dattijuwa yar shekara 80 fyade a jihar ta Kano.

Ko a farkon watan da ya gabata, wata yarinya mai shekara 12 ta shaida wa 'yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.

Kazalika a dai baya-bayan nan, an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami'a bayan sun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.

Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.