Shamima Begum: Matar da ta dawo daga rakiyar 'yan IS ta yi nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara

An wallafa

Alkalai a London sun yanke hukunci cewa Shamima Begum, wadda ta bar Burtaniya a lokacin tana 'yar makaranta ta je ta mara wa 'yan kungiyar IS baya a Syria, za ta iya komawa ta kalubalanci gwamnati a kan matakin soke kasancewarta 'yar asalin Burtaniya.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta ce ba a ba ta damar gabatar da korafinta daga sansanin da take a arewacin Syria ba inda ake tsare da ita a can.

Shamima mai shekara 20 a yanzu, na daya daga cikin 'yan mata 'yan makaranta uku da suka bar Landan don shiga kungiyar IS a shekarar 2015.

Tun tana shekara 15 ta yi wasu abubuwa na fitina wadanda taga baya aka zo aka kamata da laifin aikata su.

Yanzu haka dai ta yi aure inda ta auri wani dan IS din har suka samu 'ya'ya uku wadanda dukkan su a yanzu sun mutu. Tuni dai gwamnatin Burtaniya ta yi Allah-wadai da hukuncin kotun inda ta bukaci damar daukaka kara.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida na kasar ce ta kwace shaidar zamanta 'yar Burtaniya kan hujjojin tsaro bayan da aka gano ta a wani sansani a 2019.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce an ki sauraron kararta ne sanoda ba ta iya gabatar da hujjoji daga sansaninta na Syria ba.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce hukuncin kotun bai yi mata dadi ba kuma za ta daukaka kara.

Hukuncin na nufin dole a yanzu gwamnati ta samo hanyar barin matashiyar, wacce a yanzu take Sansanin Roj a arewacin Syria, ta bayyana a gaban kotu a Landan duk da ta sha maimaita cewa ba za ta taimaka wajen fitar da ita daga Syria ba.

Masu Shari'a Lord Justice Flaux da Justice King da kuma Lord Justice Singh - sun ce: "Dole a yi adalci a kan lamarin nan wajen ganin rinjayi fargabar samar da tsaro ta hanyar ba ta damar shiga kasar don ta bayyana a gaban kotu.

Mai shari'ar ya kuma ce za a warware matsalar damuwar da ake da ita a kan tsaron idan har ta koma Burtaniyan.

Mene ne dalilin mata na shiga kungiyoyin jihadi?

Akwai dalilai da dama da ke jan mata su shiga irin wadannan kungiyoyin.

Lamarin ya kai ga cewa abin da ke ingiza maza shi ke ingiza mata, kamar al'amuran da suka hada da jan ra'ayin akida da fa'idar samun kudi.

Sai dai dabarun da ake tunkarar mata da su musamman, su ne jan ra'ayinsu da cewa za su koma rayuwar al'adar matsayin bambanta jinsuna (matsayin mata da maza daban-daban).

Alal misali, daya daga bincikenmu ya nuna cewa masu jawo mutane cikin kungiyar al-Shabab sukan fake da damar rashin kariyar tsaro ga matasan mata Musulmi, wadanda ke fargabar cewa karatu a manyan makarantu zai kawo musu cikas din yin aure a kan kari.

"Idan na samu mutumin da zai aure ni ya ba ni kariya (kula da ni), mene ne zai sanya in damu kaina da zurfin karatu?" a cewar wata dalibar Jami'ar Nairobi da masu binciken suka tuntuba.

Sauran kuwa an gano cewa al'amuran da suka dauki hankalinsu su ne alkawuran samun aikin yi da kudi da sauran damarmaki a fagen rayuwa.

Amma dai zakulo hakikanin manufarsu ta shiga kungiyoyin na da wahala.

Mata da dama da aka tattauna da su sun yi ikirarin cewa an shigar da su kungiyoyin ne ba a son ransu ba.

Kamar ita Shamima Begum , wasu sun yi ikirarin cewa ba sa yin fafutika a harkokin kungiyar, ko kuma shiga a dama da su ba da son ran su ba, wasu kuwa cewa suka yi tsautsayi ne ya afka musu.

Yayin da wasu ke nuni da cewa akwai yiwuwar tursasasu aka yi suka shiga harkokin kungiyar ta wata siga, inda suka musanta suna da alhakin aikata munanan ayyuka, wannan hanya ce mai alfanu wajen dawo da su cikin al'umma.

Hanyar gyara dabi'a

Akwai dabaru da dama na tarbiyyar gyaran dabi'a ga wadanda suka samu kan su a kungiyoyin a da ko dawo da mayakan kan hanya tagari, amma kadan ne aka tsara su da nufin tarairayar mata.

Masu tsara muhimman dabaru da harkokin tsaro na bukatar tunkarar al'amuran da suka shafi mata don ganin an shawo kan su sun yi watsi da kungiyoyin ta'addanci, ta yadda za a kare aukuwar lamarin da gyaran tarbiyya da dabarun sake dawowarsu cikin al'umma.

Alal misali, da yawansu sun haifi 'ya'ya da mayakan da suka mutu ko suka arce daga fagen daga, yayin da wasunsu ke bukatar tarairayar tarbiya da shawo kan yadda za su shawo kan matsanancin halin da suka tsinci kan su a ciki, kan al'amuran da suka kama daga kan fyade zuwa cin zarafinsu ta hanyar tarawar jima'i.

Yana da matukar muhimmanci gwamnatoci su shawo kan al'amuran da suka shafi matan da suka tsunduma a harkokin kungiyoyin ta'addanci.

Lamarin zai fara ne daga kan yadda za a samar da kyakkyawar fahimta kan bambance-bambancen jinsuna da ke ingiza mata, tare da al'amarin da ke da tasiri kan rayuwarsu.

Yin hakan zai yi matukar taimaka wa al'ummomi su tarairayi hadarin da ake fama da shi, kuma ya taimaka wajen dakilewa ko hana karuwar matan da ke shiga kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayin ta'addanci.