Rikicin Yammacin Kogin Jordan: Ana zanga-zangar tir da Isra'ila

An wallafa

Dubban mutane na gudanar da zanga-zanga a Gaza, domin nuna rashin amincewa da shirin Isra'ila na mamaye yankin gaɓar yamma da Kogin Jordan.

Masu boren na ɗaga tutocin Falasdinawa, suna kuma yin Allah wadai da Shugaba Trump na Amurka kan goyon bayan da ya nuna ga shirin Isra'ilar.

Shi ma Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya gargaɗi Isra'ila da ta watsar da shirin nata da ake hangen zai tayar da sabon rikici a yankin.

Wakilin BBC ya ce kusan dukkan kawayen Isra'ila sun ce shirin na mamayar da take yi ba da yawun bakinsu ba. Dama kuma kasar na cikin rudun siyasa''.

To sai dai gwamnatin Benyamin Netanyahu ta ce a ranar Laraba ne za ta fara abin da ta tsara.

Me Boris Johnson ya ce?

Tun da fari a aranar Laraba, Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya nemi Isra'ila da ta dakatar da shirinta na mamayar wani bangare na Gabar Yamma da Kogin Jordan, yana mai cewa hakan ba ya kan doka kuma sabanin manufar kasar ne.

Takwaransa na Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sanya yau Laraba a matsayin ranar da Isra'ila za ta fara jaddada ikonta kan yankunan Yahudawa da ke Gabar Yamma da Kogin Jordan.

Sai dai da alama wannan shiri ya fuskanci cikas.

Falastinawa sun ce matakin zai rusa burinsu na samun tabbatacciyar kasa.

Matakin na Isra'ila zai yi dai-dai da kudirin Shugaba Donald Trump na zaman lafiya - matakin da zai kawo karshen tsawon shekarun da aka shafe ana rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa da ya kaddamar cikin watan Janairu.

Yahudawa 430,000 ne ke zaune a yankuna sama da 130 da aka gina, amma tun bayan da Isra'ila ta mamaye Yammacin Kogin Jordan a yakin Gabas Ta Tsakiya da aka yi a 1967.

Ana yi wa yankunan kallon haramtattu karkashin dokokin kasashen duniya duk da Isra'ila - da Amurka karkashin mulkin Trump - sun musanta hakan.