Shin za a kawo ƙarshen 'Yaƙi da Ta'addanci' kuwa?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Frank Gardner
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC security correspondent
- An wallafa
Ƙazamin harin wuka da aka kai Reading a yammacin Landan kwanakin baya na ci gaba da tunasar da jama'a barazanar harin ta'addanci da aka manta da shi. Amma ina batun yaki da ta'addanci, da tsohon Shugaba George W. Bush ya kaddamar a 2001? Har yanzu akwai shi? Idan an daina, to hakan na nufi an yi asarar kudi kenan?
Kusan shekaru 19 da harin ranar 11 ga watan Satumba 2001 a Amurka dubban dakarun Amurka - mata da maza - ke jibge a Afghanistan da Iraqi da yankin Gulf da wasu yankunan Afirka. Hare-haren da ake kai wa da jirage marasa matuka a kananan kauyuka da shugabannin 'yan ta'adda ke maboya, harin kwanton-bauna da ake kai wa a yankunan da dama a duniya na sake nuna irin barazanar da ke karuwa a duniyar.
Sasha Havliclek, shugabar cibiyar nazari kan sulhu, ta jima tana bibiyar wannan yaki tun asalinsa. Kuma ta jaddada cewa akwai bambanci tsakanin hasashe da kuma abin da ke a bayyane:
'Makiya masu kafiya'
Wannan shi ne ra'ayin mutumin da Shugaba Donald Trump ya nada a ma'aikatar tsaron cikin gida domin yakar ta'addanci, Ambasada Nathan Sales. Na tambaye shi cewa wannan yaki - da aka soma tun zamanin Bush - ya kare?
"A'a, har yanzu ana kan wannan yakin, muna samun galaba a wannan yaki sai dai muna ci gaba da yaki da makiya da ke da kafiya ko na ce kungiyar makiya masu naci."

Asalin hoton, Reuters
Ya bayar da misali da mayakan masu ikirarin Jihadi na IS wanda hadaka ko kawancen dakaru daga sassa daban-daban suka yi nasarar kakkabe su daga Syria a shekarar da ta wuce, haka ma shugabanta Abu Bakr Al-Baghdadi. Amma har yanzu wannan kungiya ba ta gushe ko kare a doron-kasa ba, har yanzu tana aikata muggan ayyuka.
A ranar Laraba, hukumar tsaro ta Amurka ta fitar da rahoton shekara kan yaki da ta'addanci.
Ga wasu a Washington, komai kusan ya wuce kan harin ranar 9/11 da aka kai Amurka.
A lokacin sanar da soma yaki da ta'addaci a wancan lokacin, Shugaba Bush ya sanar da cewa "kana da zabin ba mu hadin-kai ko bijire mana". Babu batun shiga tsakani, babu alawus da aka ware ga gabas ta tsakiya da kawance da suka samu.
Kutsawar Amurka da Burtaniya Iraqi a shekara ta 2003, ta tilas ko taka rawa wajen haifar da gaba da kiyayya, da taka rawa wajen jefa duniya halin da ake ciki a yanzu na ta'addanci. Mina Al-Orabi ita ce shugabar jaridar UAE. 'Yar asalin Mosul ce na Iraqi, wanda yaki da IS ya lalata tarihinsa.
"Ta ce a Iraqi, akwai lokutan da Amurka ta rinka yi wa kasar dan-waken zagaye. A 2003 ta yanke hukunci tarwatsa 'yan sandanta da sojoji, shawarar da ya jefa dubbai cikin rashin aikin yi...an yi tunanin hakan zai sa a ware su daga kasar, wannan ya bude kofa kuma ya assasa kungiyoyin jihadi irin su al-Qaeda da IS zame wa duniya barazana."
'Akwai sauran aiki'
Wasu daga cikin irin kura-kuran da aka aikata wadanda kuma suka bude kofa ga yaki, akwai wasu matakai na Shugaba Obama, da yau ake girbe abin da ya shuka.
Garkame dubban mutane ba tare da an yi musu shari'a ba a gidan yarin Guantanamo Bay, ana rufe idon dan ta'adda ba tare da ya fahimci inda za a kai shi ba, kuma a sanya mutum cikin azaba.
Wannan wani salon yaki ne da aka jima ana sukarsa da kasashen yamma ke amfani da shi. Ambasada Sale daga ma'aikatar tsaro na Amurka ya ce "duniya ta koyi darussa kan abubuwa da suke aiki da wadanda ba sa aiki wajen tunkarar irin wadanan matsaloli".
Yana cikin mutanen da ke kyamar Guantanamo Bay, da ayyukan Amurka da kawayenta, da yanzu haka suka mantar da 'yan kasarsu a wannan sansani da kuma a Syria da Iraqi. Ya ce akwai bukatar wadannan kasashe su dawo da 'yan kasarsu.
Abu ne mai wahala a iya gane adadin kudade da wannan yaki da ta'addanci ya lakume amma dai Amurka ta kashe sama da dala triliyan guda.
"Idan aka dubi abubuwan da ke faruwa na IS da Syria da Iraqi," a cewarsa "to wannan watakila baya rasa nasaba da kyamar da ake fuskanta a Turai, da suka danganci nuna kiyayya ga Musulmi, rikicin 'yan gudun hijira Syria. Wadannan duk tasiri abubuwa da ake aikatawa ne da babu dacewa a ciki. Don haka ana iya cewa yaki da ta'addanci ba abu ne da zai kare nan kusa ba ne."










