Lafiya Zinariya: Abin da ba ku sani ba a kan ƙabar mahaifa

Bayanan sautiLafiya Zinariya: Abin da ba ku sani ba a kan ƙabar mahaifa
An wallafa

Ƙabar Mahaifa na ɗaya daga cikin cututtukan da suka fi shafar mata da shekarunsu suka kai na haihuwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mata miliyan 235 cutar ke shafa a duniya.

A wannan makon, mun tattauna da wata wadda ta taɓa fama da fibroid kuma ta bayyana mana yadda cutar ta hana ta walwala.

Sannan likitar mata Dakta Ashiyya Siddiqi ta yi mana cikakken bayani dangane da cutar.