Moscow: Hotunan bikin tunawa da nasarar 'yan Soviet kan sojojin Nazi

An wallafa

Shekara 75 ke nan tun da tsohuwar Tarayyar Soviet ta sami galaba kan sojojin Nazi a Yakin Duniya na Biyu da ya lakume rayukan 'yan kasar ta Soviet fiye da miliyan 20.

Russian servicemen march in the Victory Day Parade in Red Square in Moscow, Russia, June 24, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dubban sojojin Rasha sun yi maci a ranar tunawa da nasarar tsohuwar kasar Soviet kan sojojin Nazin Jamus a dandalin Red Square na birnin Moscow
Vintage T-34 tanks rehearsing in Moscow, 20 Jun 20

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, An baje kolin tsofaffin tankokin yaki samfurin T-34 wadanda sojojin Soviet suka rika amfani da su yayin Yakin Duniya na Biyu
President Putin during the World War Two victory parade

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban Rasha Vladmir Putin ya so a yi bikin a farkon watan Mayu amma annobar korona ta hana
Russ

Asalin hoton, AFP PHOTO/Host photo agency/Mikhail Voskresens

Bayanan hoto, Yadda sojojin rundunonin sojojin Rasha suka yi fareti mai kayatarwa a dandalin Red Square na Moscow
Russian servicemen march before the Victory Day Parade in Red Square in Moscow, Russia, June 24, 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojojin Rasha da na wasu makwabtan kasashe sun yi fareti tare a filin Red Square na birnin Moscow
Russian servicemen march in the Victory Day Parade in Red Square in Moscow, Russia, June 24, 2020

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An nuna daruruwan motocin yaki na da da na yanzu yayin faretin da aka yi a dandalin Red Square
Veteran salutes during World War Two victory parade

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Ba a bar tsofaffin sojojin Tarayyar Soviet da suka yaki 'yan Nazi yayin Yakin Duniya na Biyu a baya ba
Russian servicemen march in the Victory Day Parade in Red Square in Moscow, Russia, June 24, 2020

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Fiye da sojojin Rasha 13,000 ne suka shiga kasaitaccen faretin a dandalin Red Square
Pilots fly over Red Square for the Victory Day parade

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jiragen yaki na Rasha sun rika shawage a sararin samaniyar Moscow inda suka rika yin feshin launukan tutar kasar Rasha