Kara Bridge: Tankar mai ta kama da wuta a Lagos

Fashewar tanka a Legas

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Wata tankar mai ta kama da wuta a kan wata babbar gada da ake kira Kara bridge a Legas kudancin Najeriya.

Rahotanni sun ce wutar ta yadu inda ta sake kama wata tankar mai da ke kusa da ita mai dauke da fetir.

Tuni dai 'yan kwana-kwana suka isa wajen domin kashe wutar da rahotanni suka ce ta ci motoci da gidajen da ke kusa.

Zuwa yanzu ba a tantance musabbabin faruwar lamarin ba, da kuma hasarar rayuka da dukiyoyi da fashewar ta janyo.

Muna tafe da karin bayani