Coronavirus a Abuja: Yadda cutar korona ta sauya tsarin Sallar Juma'a

Bayanan bidiyo, Yadda cutar korona ta sauya yadda ake Sallar Juma'a
An wallafa

Kasashen duniya daban-daban na ci gaba da sassauta matakan da suka dauka na takaita yaduwar cutar korona.

A Najeriya musulmi sun shafe tsawon watan Ramadan mai falala cikin dokar kulle, ba tare da zuwa masallatai da kuma tarukan bude-baki ba.

To yanzu da ake bude wuraren ibada, wanne darasi suka dauka game da rufe wuraren ibadar da aka yi tun farko?

Kuma mene ne ya sauya game da abubuwa da suka saba yi a wuraren ibada?

Wata musulma da ta saba zuwa masallaci, Habiba Musa Ahmad, ta yi mana karin bayani a Masallacin Othman Ibn Affan da ke Abuja.