Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Trump ya zargi Twitter da hana shi 'yancinsa
Shugaba Trump ya soki Twitter da hana shi 'yancin fadin albarkacin baki bayan a karon farko shafin ya bayyana wani sako da shugaban ya wallafa a matsayin na yaudara.
Wannan yaki da Twitter ya soma ne lokacin da Mista Trump mai mabiya sama da miliyan 80 ya yi ikirarin cewa amfani da wasiku wajen kada kuri'a a zaben kasar da ke tafe zai haddasa mummunan magudin zabe.
Kamfanin Twitter ya mayar da martani ta hanyar tura wa mutane wani shafi da ke dauke da makala ta musamman da cikakkun bayanai da ke karyata ikirarin shugaban.
A farkon wannan watan Twitter ta fito da sabon tsarin dakile bayanan karya, wanda ke taimakawa wajen ganon sahihancin labarai musamman a kan cutar korona.