'Na yi asarar fiye da N200m sakamakon cutar korona'

Bayanan bidiyo, 'Na yi asarar fiye da N200m sakamakon cutar korona'
An wallafa

Wani dan kasuwar jihar Kano da ke Najeriya, wanda yake kasuwancin auduga zuwa kasashen waje, ya shaida wa BBC cewa cutar korona ta sa ya yi asarar fiye da Naira miliyan 200.

Alhaji Rabi'u Abdullahi Ibrahim ya ce yana sana'ar auduga zuwa kasashe irin su China da Spaniya da Italiya, yana mai cewa bullar cutar korona ta sa kasuwancin nasa ya tsaya cak.

Ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta tallafawa 'yan kasuwar kamar sa domin su farfado daga halin da suka trsinci kansu a ciki.