Coronavirus: Galibin masu cutar a Jigawa almajirai ne

@SankaraJgh

Asalin hoton, @SankaraJgh

An wallafa

Gwamnatin jihar Jigawa ta ce fiye da rabin mutanen da suka kamu da cutar korona a jihar kananan yara ne almajirai da wasu jihohi makwabta suka mayar musu.

Alkaluman hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta Najeriya sun nuna cewa Jigawa ta samu karin masu korona 23 a ranar Laraba 13 ga watan Mayu, inda adadin masu cutar ya kai mutum 141 a jihar.

Jigawa na daga cikin jihohin kasar da aka samu hauhawar masu fama da wannan annoba kuma zuwa yanzu tana kan mataki na bakwai tsakanin jiha 34 da kuma babban birnin kasar Abuja.

A zantawarsa da BBC ta wayar tarho, Gwamnan Jigawa Badaru Abubakar ya ce a cikin adadin akwai almajirai guda 63 zuwa 64 da gwaji ya tabbatar suna da korona bayan Kano ta mayar da su jihar.

Ya ce tuni suka kammala gwada almajirai sama da 400 a cikin wadanda aka mayar musu daga Kano kimanin 600.

A cewar Gwamna Badaru sauran almajiran da aka tantance kuma aka ga ba su da wannan cuta, tuni suka mayar da su hannun iyayensu, bayan yi musu rijista a makarantun boko.

"A yanzu dai (duka-duka) an kawo mana yara kusan 1, 100 yanzu amma mun fara aiki a kan wadanda aka kawo daga Kano su kusan 600," in ji Gwamna Badaru

Badaru Abubakar ya ce nan da 'yan kwanaki za su sake daukar samfur din masu cutar don a sake gwada ta yadda za a tantance ko cutar ta rabu da su ko kuma suna bukatar ci gaba da jinya.

A kwanan baya ma sai da gwamnan jihar Kaduna Nasir Elrufa'i ya ce sun samu karin mutum 19 masu cutar korona, al'amarin da ya kara yawan adadin masu cutar a jihar daga 9 zuwa 25.

El-rufa'i wanda ya wallafa bayanin a shafinsa na Tiwita, ya ce sun yi wa almajirai 40 gwaji, inda sakamakon 19 daga cikinsu ya nuna suna dauke da korona.

Malam Nasir El-Rufai

Asalin hoton, @GovKaduna

Bayanan hoto, Jihar Kano ta mayar da almajirai da dama jihohinsu na asali

Gwamna Elrufa'i ya kuma ce yanzu ta tabbata shige da fice da ake yi wa jihar tasa ne ke janyo karuwa masu cutar a Kaduna, inda ya ja hankalin jami'an tsaro su ci gaba da sanya ido kan duk masu shiga birnin ta barauniyar hanya.

Ko a makon da ya gabata ma sai da gwamnan ya sanar cewa sun samu biyar daga cikin almajiran da aka mayar wa jihar tasa daga Kano da cutar korona.

Kididdiga dai ta nuna akwai almajirai miliyan tara a yankin arewacin Najeriya, abin da ya sa ake fargabar yaran suna iya yada cutar matukar wasu daga cikinsu sun kamu da ita.

Za a iya cewa wannan ne karon farko da gwamnatocin jihohin arewacin Najeriyar ke kokarin kwashe almajiran da ke jihohinsu suna mayar da su jihohinsu na asali.

@SankaraJgh

Asalin hoton, @SankaraJgh

Almajirai

Asalin hoton, Getty Images

Ita dai gwamnatin Kano kokarinta na dakile bazuwar korona a birnin Kano ne, ya sanya Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bullo da shirin mayar da almajirai jihohinsu da suka fito.

Masana harkar lafiya da dama sun soki lamirin shirin bisa hujjar cewa hakan na iya fantsama cutar a wasu jihohin da ba su da ita.

Tun ranar 22 ga watan Afrilu ne gwamnonin jihohin arewacin Najeriya 19 suka sanar da rufe dukkanin makarantun tsangaya kuma babu jimawa gwamnatin Kano ta fara mayar da almajiran makarantun zuwa jihohinsu na asali.