Na shafe kwana 40 a killace saboda cutar korona - Muhammad Atiku

Bayanan bidiyo, Muhammad Atiku Abubakar
An wallafa

Latsa wannan hoto na sama domin sauraron hirar Muhammad Atiku da Salihu Adamu

Dan gidan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Muhammad Atiku Atiku ya ce babban darasin da ya samu a cibiyar da aka killace shi ta masu fama da cutar korona da ke Abuja, shi ne bai wa kowanne dan adam girman da Allah ya ba shi.

Muhammad Atiku wanda ya kwashe kimanin kwanaki 40 a cibiyar, ya ce bai san dalilin da ya sa ya kwashe lokaci mai tsawo a cibiyar ba yana jinya duk kuwa da cewa babu alamar ciwo a tare da shi.

Ya kara da cewa zaman a cibiyar killacewar tamkar zama a gida ne domin mutum zai yi amfani da wayarsa da kwamfuta sannan har ma a ziyarce shi amma daga nesa-nesa.