'Yan Kannywood na jimamin mutuwar Ubale Wanke-Wanke

Bayanan bidiyo, Daga Bakin mai ita tare da Ubali Ibrahim
An wallafa

Masu fitowa a fina-finan Hausa na Kannywood suna ta mika ta'aziyarsu tare da jimamin mutuwar abokin aikinsu Ubale Ibrahimda aka fi sani da Ubale Wanke-Wanke.

Ubale ya rasu ne ranar Alhamis da yamma a Kano, kuma tuni aka yi jana'izarsa a ranar Juma'a da misalin karfe takwas na safe a Rangaza, a Kano.

Ubale ya shafe tsawon lokaci yana fama da hawan jini da ciwon zuciya da suke yawan taso masa akai-akai.

Mansura Isah matar Sani Danja ta shaida wa BBC cewa ''Sai dai a wannan karon da ciwon ya tashi sai ya zama jalinsa.

''Ba mu taba tsammanin cewa ba zai tashi ba, mun zaci ciwon zai yi sauki kamar yadda ya saba tashi ya kuma lafa tsawon shekaru,'' in ji ta.

Sani Danja da matarsa Mansura wadanda su ne iyayen gidan Ubale a masana'antar su ne suka fara sanar da mutuwar tasa a shafukansu na sada zumunta.

Taurarin Kannywood kamar su Ali Nuhu da Yakubu Mummahd da Rahama Sadau da Maryam Booth da Falalu Dorayi da kuma Ado Gwanja duk sun wallafa sakon ta'aziyyarsu da jimami a shafukansu na Instagram.

Duk da cewa Ubale ya dade a harkar Kannywood, amma bai shahara sosai ba, kuma bai yi wasu tarin fina-finan masu yawa ba.

Kazalika Ubale ya fi fitowa ne a fina-finan kamfanin Sani Danja, amma ya kan fito a wasu ma jefi-jefi, sai dai ya shafe lokaci ba ya fitowa a fim a baya-bayan nan.

''Ya dade bai yi fim ba gaskiya, sai dai muna aiki tare a kungiyar NGO dita da muke taimaka wa marasa galihu,'' in ji Ansura.

Ubale dan asalin Unguwar Tudun Murtala ne a birnin Kano. Ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya shida.