Covid-19: Shah Rukh Khan zai bai wa ma'aikatan lafiya gudunmawar kayan kariya

An wallafa

Fitaccen tauraron fina-finan India, Shah Rukh Khan, ya ce zai bayar da kayan kariya 25,000 ga ma'aikatan lafiyar da ke fafutukar dakile yaduwar cutar korona a jihar Maharashtra da ke yammacin kasar.

An yi ta watsa labarai kan tauraron mai shekara 54 watan jiya bayan ya sanar da daukar matakai daban-daban wadanda za su taimaka wajen dakile cutar a India, ciki har da bayar da abinci kyauta da kuma zai bayar da ofishinsa domin a yi amfani da shi wajen jinyar mutane da ska kamu da Covid-19.

Shah Rukh Khan yana cikin shahararrun mutanen da ake girmamawa a India kuma ya fito a fina-finai fiye da 90.

Mutum 339 ne suka mutu a India sanadin cutukan da ke da alaka da korona.