Coronavirus: Magungunan bogi sun karu saboda annobar

- Marubuci, Daga Sam Piranty
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- An wallafa
A fadin duniya, mutane na sayen magunguna suna jibgewa. Amma, yayin da manyan kasashen da ke samar da magunguna a duniya - China da Indiya- suka dakatar da duk wasu ayyuka a cikinsu, bukatar magungunan a yanzu ta fi yawan yadda ake samar da shi kuma sayar da magungunan bogi na karuwa.
A makon da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ayyana coronavirus a matsayin annobar duniya, Operation Pangea, wani bangare na jami'an tsaro na kasa da kasa da ke yaki da laifukan sayarwa da samar da magunguna, ya kama mutane 121 a kasashe 90 a cikin kwanaki bakwai.
Sanadiyyar haka, an kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai sama da dala miliyan 14.
Daga Malaysia zuwa Mozambique, 'yan sanda sun kwace dubban takunkuman fuska na bogi da magungunan bogi, da yawa daga cikinsu kuma na cewa suna maganin coronavirus.

Asalin hoton, Getty Images
"Saye da sayar da magunguna ba a bisa ka'ida ba a wannan yanayi na annoba na nuna rashin ganin kimar rayuwar dan Adam," in ji Sakatare Janar na Jami'an tsaro na kasa da kasa Jurgen Stock.
A cewar WHO, kasuwar magungunan bogi, wadda ta kunshi magungunan da ka iya zama gurbatattu ko kuma wadanda suke dauke da sinadaren da ba su dace ba ko sinadaren da suka lalace, ta kai dala biliyan 30 a kasashe masu karanci da matsakaicin tattalin arziki.
"Idan aka sha magungunan bogi, ba lallai su magance cutar da ake so a kawar ba", in ji Pernette Bourdillion Esteve, jami'ar WHO da ke aiki da magungunan bogi.
"Haka kuma, suna iya janyo illa saboda akwai yiwuwar suna dauke da wata guba."


Yadda ake sa magungunan a kasuwa
Arzikin kasuwar magunguna ta duniya ya kai sama da dala triliyan daya.
Jerin matakan samar da magungunan suna da yawa kama daga masu sarrafawa a wurare kamar China da India zuwa inda ake sa shi a kwalaye ko kwalabe a Turai da Amurka ta Kudu ko Asiya, zuwa 'yan kasuwa da ke aika magungunan zuwa ko wace kasa ta duniya.
"Ana iya cewa babu abin da ya kai magunguna hada kan duniya" in ji Esteve.
Sai dai, yayin da duniyar ta tsaya cik, jerin matakan samar da magunguna sun fara watsewa.
Kamfanonin samar da magunguna da yawa a India sun shaida wa BBC cewa yanzu suna kashi 50-60 cikin 100 ne kawai na ayyukansu.
Yayin da kamfanonin Indiya ke samar da kasha 20 cikin dari na duka magungunan a nahiyar Afrika, lamarin zai matukar shafar kasashen Afrika.

Ephraim Phiri, wani kwararre kan harhada magunguna a Lusaka, Zambia ya ce ya fara ganin haka.
''Magunguna sun fara karewa kuma ba ma iya samun wanda za su maye gurbinsu.
''Ba yadda za mu yi. Da matukar wahala samun magunguna…. Musamman magunguna masu muhimmanci kamar magungunan maleriya.''
Masu samarwa da manyan 'yan kasuwa na fama saboda abubuwan da ake bukata wajen samar da magungunan sun yi tsada yanzu, wasu kamfanonin ma ba su da kudin sayen kayan.
Wani mai samar da magunguna a Pakistan ya ce a baya, yana sayen kayan hada magungunan wani maganin maleriya mai suna hydroxychloroquine kan kusan dala dari duk kilo.
Amma yanzu, ya ce kudin kayan ya kai dala 1150 kan ko wane kilo.

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da yawan kasashen da ke dakatar da ayyuka cik ke karuwa, ba raguwar samar da magungunan ce kawai matsala ba, bukatar magungunan za ta karu yayin da mutane a fadin duniya ke ta rububin sayen magungunan yau da kullum suna jibgewa.
Wannan yanayin ne, na ragi a samar da magungunan da kuma karuwar bukatarsu, WHO ta yi gargadin kan karuwar samarwa da sayar da magungunan bogi.
"Idan samarwar ta gaza cimma yawan bukatar", in ji Esteve, tana haifar da wani yanayi inda magungunan bogi za su yi tasiri wajen cimma wannan bukata."
Maganin Bogi
Da muka yi Magana da masu sarrafa magunguna da kamfanonin da ke samar da magunguna a fadin duniya, samar da magungunan maleriya a fadin duniya na fuskantar barazana yanzu.
Tun da Shugaba Trump ya fara magana kan yiwuwar chloroquine da hydroxychloroquine na maganin coronavirus a tarukan manema labarai a fadar White House, an samu karuwar bukatar magungunan a fadin duniya, wanda aka saba sha don magance zazzabin maleriya.

Karin labaran da za ku so ku karanta

WHO ta sha ambaton cewa babu wata takamaimiyar shaida da ke nuna cewa chloroquine ko hydroxychloroquine na iya kawar da kwayar cutar da ke janyo Covid-19.
Sai dai a wani taro na kwanan nan, a lokacin da yake maganar wadannan magungunan na maleriya, Shugaba Trump y ace: "Me zai hana ba za a gwada ba? A gwada."
Yayin da bukatar magungunan ke karuwa, BBC ta gano cewa akwai chloroquine na bogi sosai a kasuwa a Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo da Kamaru.
An saba sayar da robarsa guda mai dauke kwayoyi 1000 kusan dala 40, amma a shagunan sayar da magunguna a Jamhuriyar Demokradiiyar Congo an gano suna sayar da chloroquine har dala 250.
An samar da maganin da ake siyarwar ne a Belgium, a wani kamfani mai suna Browb and Burk Pharmaceutical kimited.

Amma da muka nemi jin ta bakin kamfanin, wanda aka yi wa rajista a Burtaniya, sai suka ce bas u da "hannu a samar da maganin. Ba mu muke samar da wannan maganin ba, na bogi ne."
Yayin da annobar coronavirus ke ci gaba, Farfesa Paul Newton, wani kwararre a bangaren magungunan bogi a Jami'ar Oxford, ya yi gargadin cewa sayar da magungunan bogi zai ci gaba har sai gwamnatoci sun hada kai don yaki da shi.
"Akwai hadarin afkawa wata annobar, ta magungunan bogi idan har ba mu tabbatar da cewa mun samar da wani tsari na yaki da shi ba a fadin duniya…. Idan ba haka ba kuwa za a yi asarar amfanin ilimin kiwon lafiya na zamani."
Jilla Dastmalci ce ta yi zanen da ke cikin labarin nan










