Coronavirus: Yadda masallatan Abuja suka kasance ranar Juma'a

An wallafa

Kamar wasu birane da jihohin Najeriya, masallatan juma'a a babban birnin kasar, Abuja sun kasance fayau ba tare da jama'a sakamakon umarnin gwamnati.

Masallacin Abuja
Bayanan hoto, Farfajiyar babban masallacin birnin Abuja ta kasance fayau, da misalin karfe 2:30 na ranar Juma'a ta 27 ga watan Maris 2020.
Babban masallacin Abuja
Bayanan hoto, Nan ma wani bangare ne na babban masallacin Abujar inda kafin yanzu samun wuri a masallacin ga mutumin da ya je a makare to da abu ne mai wuya.
Babban masallacin Abuja
Bayanan hoto, Daya daga cikin kofofin shiga babban masallacin Abuja ta kasance a kulle a ranar Juma'a 27 ga watan Maris na 2020.
Abuja
Bayanan hoto, Filin da motoci suke yi fakin kenan a babban masallacin na Abuja amma a wannan juma'ar wurin ya kasance fayau.
Abuja
Bayanan hoto, Masallacin Annur da ke Wuse 11 a Abuja wanda shi ma ya kasance a kulle sabanin yadda yake a baya, kafin bayyanar cutar coronavirus.
Abuja
Bayanan hoto, Kofar shiga masallacin Annur kenan inda ta kasance a kulle.
Abuja
Bayanan hoto, Nan gefen masallaci na Annur ne inda jama'a ke kafa sahu idan cikin masallacin ya cika.
Abuja
Bayanan hoto, Rumfar da jama'a ke kafa sahu idan cikin masallacin ya cika makil.
Abuja
Bayanan hoto, Nan ma rumfa ce da jama'a ke sallah a masallacin Annur, a duk lokacin da cikin masallacin ya cunkushe.
Masallacin Annur
Bayanan hoto, Kantar ajiye takalma da ke wajen masallacin Annur ta kasance fayau a ranar 27 ga Maris 2020.