Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yarima Charles ya kamu da coronavirus
Yarima Charles - wanda shi ne babban dan Sarauniya Elizabeth ya kamu da cutar coronavirus.
Yariman mai shekaru 71 ya soma samun kulawar likitoci.
Ya nuna alamun cutar amma kuma yana cikin koshin lafiya.
A wata sanarwa da fadar sarauniyar Ingila ta fitar, ta ce "ya dade yana nuna alamun cutar amma kuma yana cikin koshin lafiya inda yake gudanar da ayyukansa daga gida a 'yan kwanakin da suka gabata."
Mai magana da yawun fadar ya ce "mai dakin Yarima Charles ta yi gwaji amma kuma ba ta dauke da cutar ba."
Sai dai sanarwar ta kara da cewa "babu wani tabbaci na inda Yarima ya samo cutar ta coronavirus sakamakon irin gogayyar da ya yi da mutane da dama a 'yan makonnin da suka gabata."
Yanzu haka dai Prince Charles da mai dakinsa na killace a gidansu da ke Scotland.