Abin da yasa kotu ta bar Oshimhole ci gaba da jan ragamar APC

Wata Kotun Daukaka Kara a babban birnin Najeriya Abuja ta ba da umarnin jingine hukuncin wata kotun tarayya ta mai shari'a Danlami Senchi, wanda ya dakatar da Adams Oshimhole daga shugabancin jam'iyyar APC.
Oshimhole dai ya garzaya kotun ne, inda ya kalubalanci hukuncin da kotun tarayya ta yi tun da farko.
Rikicin shugabanci ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.
Kotun mai alkalai uku, karkashin jagorancin Mai Shari'a Abubakar Yahaya ta ce sai an jingine hukuncin da kotun baya ta yi na dakatar da Oshimhole ne, sannan zai samu damar ci gaba da jagorantar jam'iyyar.
Don haka ne shi jagoran alkalan, Mai shari'a Abubakar Yahaya ya tabbatar da jingine hukuncin dakatarwar da babbar kotun baya ta yi har zuwa lokacin da kotun Daukaka Karar za ta saurari karar da aka shigar ranar Juma'a, 20 ga watan nan.
Ibrahim Masari shi ne babban jami'in walwala na jam'iyyar APC wanda yana daya daga cikin masu mara wa Adams Oshimhole baya.
BBC ta tambaye ko yaya suka ji da wannan hukunci?
''Muna yi wa Allah SWT godiya da ya kara tabbatar da ikonsa. Don wasu ne a da suka dauki kwangilar ruguza APC. Kuma idan ba su yarda da abin da abin da na ce ba to su kai ni kara cewa na musu kazafi. Gwamnan EKirti na cikinsu.''
"Don haka jazaman ne shugaban jam'iyyar Adams Oshimhole ya shiga ofis gobe,'' in ji Masari.
Haka kuma kotun Daukaka Karar ta umarci dukkan bangarorin da ake shari'a da su da su martaba umarinin na ta, ta hanyar dakaktar da daukar kowanne irin mataki da ka iya shafar hukmuncin da ta yi.
To sai dai ana wata-ga-wata, wato yayin da kotun daukaka kara ke kokarin yayyafa ruwa a wannan sabata juyata, rahotanni na cewa wata babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin wucin gadi wanda zai bai wa Victor Giadom damar rikon kwaryar shugabancin jam'iyyar, domin ya jagoranci taron da jam'iyyar za ta gudanar.
APC din ta ce za kuma ta gudanar da taron kwamitin gudanarwa da aka shirya yi gobe, jim kadan bayan wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi da gwamnonin jam'iyyar APC yau a Abuja.
Rikice-rikicen shugabanci ya dabaibaye jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, inda lamarin ya kai darewarta gida biyu, abin da har ya fusata wasu jiga-jigai a jam'iyyar, irinsu Bola Ahmad Tinubu, inda yake cewa kulle-kullen siyasa ne kan zaben 2023 da wasu ke kitsawa.










