Isa Panshekara ya ce bayan Sallah zai angonce da amaryarsa Baturiya

An wallafa

Latsa hoton da ke sama don sauraron hirar saurayin baturiyar da Umar Mikail

Saurayin nan da budurwarsa 'yar Amurka ta biyo shi jihar Kano mai suna Isa Suleiman Panshekara ya ce nan da bayan Karamar Sallah zai angonce da amaryar tasa mai suna Janine Sanchez.

Saurayin mai shekara 26 ya ce sun dage shagulgulan bikin nasu ne saboda wasu dalilai ba kamar yadda ake raderadi ba a shafukan sada zumunta cewa saboda Shugaba Trump ya hana 'yan Najeriya shiga Amurka.

"Ka san komai yana iya canzawa, mun daga bikinmu zuwa mako biyu ko uku haka bayan Ramadan," Isa Suleiman Panshekara ya shaida wa BBC.

Kazalika saurayin Ba'amurkiyar ya karyata cewa annobar cutar coronavirus ce silar dage bikin, wadda ta karade sassan duniya.

Ganin cewa masoyiyar tasa mai shekara sama da 40 ta zo ta gan shi har gida kuma ta tafi, ko alaka tana nan yadda take a tsakaninsu? Sai Isa Suleiman ya ce:

"Sosai kuwa, yanzun nan kafin ka kira ni muka gama waya ta bidiyo, ka ga kuwa alama ce da ke nuna muna tare ba kamar yadda kafafen yada labarai ke fada ba."

Ya ci gaba da cewa: "Babu wani bambanci gaskiya, illa in ce ma so ne ya sake karuwa.

"Mafi yawa ta Facebook Messenger muke magana kuma waya muka fi yi ba rubutu ba (chatting) - ba kamar Instagram ba inda muka fara haduwa.

Isa Suleiman Panshekara ya ce 'yan uwa da abokan arziki na ci gaba da yi masu addu'a.

"Amma ka san ba za a rasa makiya ba, makiya kuma sai dai su je su yi ta yi," in ji shi.

Tun a watan Janairun 2020 ne dai labarin Isa da masoyiyar tasa Ba'amurkiya ya baza shafukan sada zumunta, inda wasu da dama ke tsokaci game da masoyan wadanda suke ci gaba da tsinkar furen so.

Ita dai Janine ta niki gari tun daga Amurka zuwa Najeriya domin haduwa da matashin masoyin nata, wanda ta ce "ta aminta da shi".

'Ba zan sake soyayya da 'yar Najeriya ba'

A wata hira da Isa ya yi da BBC a lokacin ya ce "a gaskiya matanmu (Hausawa) ba su iya soyayya ba" saboda suna yin sosyya ne bisa wata bukata.

"Idan baturiya ta ce tana sonka, toh tana fadin haka ne daga zuciyarta," in ji shi.

Isa wanda tsohon mai aski ne, ya ce ya dan yi fargaba a lokacin da hukumar Hisbah da DSS suka gayyace su zuwa ofishinsu.

Sai dai ya ce sun ba su shawara ne game da yadda labarin nasu yake ci gaba da daukar hankali musamman a shafukan sada zumunta.

Masoyan dai sun fara haduwa ne ta shafin Instagram a shekarar da ta gabata.