Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hanyoyin kare kai daga kamuwa da ciwon koda
Latsa alamar lasifika don sauraren hira da Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa kan ciwon koda
Yau ce ranar tunawa da cutar koda ta duniya, wadda aka kebe domin fadakar da al'umma da yunkurin rage yawan masu kamuwa da cutar da sauran dangoginta a fadin duniya.
A kan tuna da ranar ce duk Alhamis ta biyu na watan Maris.
A Najeriya wani rahoton kungiyar masu kula da lalurar Koda ta ce 'yan kasar miliyan ashirin da biyar ne ke fama da ciwo, abin da kan sa kodar ba ta aiki yadda ya kamata har sai an rika zuwa wanki.
Kididdigar da kungiyar ta fitar ta nuna cewa akasarin masu fama da cutar matasa ne.
Dakta Salihu Ibrahim Kwaifa wani kwararren likita a Najeriya, ya ce cutukan da suka fi janyo ciwon koda su ne hawan jini da ciwon suga da kuma wani nau'i na ciwon koda da ake kira CGN, wanda kuma shi ne ya fi addabar koda har ta kai ga bata aiki.
Likitan ya ce baya ga wadannan cutukan, rashin shan isasshen ruwa a lokacin gumi da amfani da magungunan feshi a kan amfanin gona da kuma gurbatar muhalli duk su kan janyo ciwon koda.
Dakta Salihu ya ce "cutar ta zama ruwan dare saboda akwai karin mutane masu cutukan hawan jini da suga da kuma an samu karuwar mutane masu shan magungunan gargajiya."
Ya ce mutane za su iya kare kansu daga kamuwa da cutar koda ta hanyar cin abinci mai gina jiki da kuma kiyaye duk abubuwan da aka ce suna janyo cutar.
"Tun mace na da ciki ya kamata ta rika cin abinci mai gina jiki sannan duk wanda ya ke da cutar da ka iya jayo ciwon koda ya kamata ya je asibiti tun da wuri a yi gwaji a tabbatar ba shi da cutar", in ji Dakta Salihu.