Malamin cocin da ke gina masallaci

Wani Malamin Cocin Orthodox da ke Habasha na tara kudi domin gina coci da masallaci a yammacin Hararge da ke yankin Oromia na kasar.
Coci da masallacin a garin Lange sun kasance cikin yanayi na rashin gyara sa'annan al'ummar garin ba su da kudin yi musu gyara.
Malamin cocin mai suna, Abba Aklilemariyam Komos ya fada wa wakilin BBC Afaan Oromoo cewa, "Allah zai yi fushi" da shi idan ya gina coci kadai ya kuma yi watsi da yanayin masallacin.
Ya samo dabarar tara kudin ne a shekarar 2015 yayin wata ziyara da ya kai garin Lange, a lokacin da ya fahimci yadda cocin garin yake.
Tuni dai ya fadada shirin ya hada da gina sabon masallaci.
Ya bayyana cewa,"idan har na tara kudi na gina coci-coci kawai alhalin masallacin 'yan uwana musulmai na bukatar hakan, Allah zai yi fushi da ni. Akidarmu ba daya ba ce, amma soyayya daya ce."
Ya sanarwa da shugabannin majalisar koli ta harkokin addinin Musuluncin Habasha da su yadda cewa da gaske yake.
"Na fara karbar kudin a watan Oktoban 2018 inda na fara zuwa masallacin Nur da ke Addis Ababa. Kafin a kai watanni biyu, mun karbi fiye da birr 200,000 na Habasha kwatankwacin dala 6,200". Inji shi.












