Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

Bayanan bidiyo, Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya
An wallafa

Latsa bidiyon sama domin kallo

Kotu ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta.

An yanke hukuncin ne bayan gurfanar da matar bisa laifin daba wa mijinta mai suna Bilyaminu Bello wuka a shekarar 2017, sakamakon rikici a tsakaninsu.

A yau Litinin ne kotun ta yanke hukuncin bayan dage zamanta a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Sanar da hukuncin ke da wuya, Maryam ta yi ta kuruwa a zauren kotu.

A baya ta musanta zargin inda ta ce mijin nata ya mutu ne sakamakon rauni da ya samu bayan ya fadi a kan kuttun shisha a gidansu.

Bidiyo: Sani Aliyu