Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kallon kwallon kafa na iya sa bugun zuciya
Wani bincike ya nuna cewa masu sha'awar kwallon kafa na fuskantar tsananin damuwa a lokacin da suke kallon tawagar da suke mara wa baya idan tana buga wasan, kuma mai yiwuwa suna jefa kansu cikin hadarin kamuwa da bugun zuciya.
Masana kimiyya a Jami'ar Oxford da ke Burtaniya sun gudanar da wani bincike kan masu goyon bayan tawagar kwallon kafa ta kasar Brazil, lokacin da Jamus ta ci su bakwai da babu a gasar cin Kofin Duniya ta shekarar 2014.
Sun gano cewar sinadarin cortisol da ke auna damuwa a jikin dan Adam ya karu sosai a lokacin da suke kallon wasan.
Idan sinadarin ya yi yawa ya kan sa jini ya hau kuma hakan na takura wa zuciya.
Masu binciken sun ce ana iya rage tasirin damuwar yayin kallon wasa ta hanyar rage karfin hasken wutar lantarki a filin wasan da kuma sanya sauti mai taushi.