Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mota ta yi kwanciyar magirbi da 'yan PDP a Abuja
Rahotanni na cewa akalla mutane hudu ne suka jikkata yayin zanga-zangar da babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP ta gudanar a babban birnin Abuja.
An gudanar da zanga-zangar a harabar kotun kolin kasar wadda a makon jiya kotun ta kwace mulki daga hannun PDP ta bai wa APC a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar..
An tayin kide-kide da raye-raye yayin zanga-zangar, haka zalika an yi ta wasa da motoci abin da ya janyo taho mu gama tsakanin motocin PDP biyu.
Lamarin ya faru ne a dai-dai sha-tale-talen da ke kan titin Shehu Shagari a birnin Abuja.
Bayanai na cewa an bar mutanen da abin ya rutsa da su a gefen titi da zimmar motar asibiti za ta kwashe su.
Ba dai a samu wani rikici ba tsakanin mabiya jam'iyya da jami'an tsaro ko kuma da mambobin wata jam'iyyar.