Africa: Zababbun hotunan karshen mako daga nahiyar Afirka

An wallafa

Zababbun kayatattun hotuna dag nahiyar Afirka a makon da ya gabata:

Wata mace 'yar Habasha tana kpokarin korar fari yayin da suke tashi a garin Jijiga ranar Lahadi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wata mace 'yar Habasha tana kpokarin korar fari yayin da suke tashi a garin Jijiga ranar Lahadi.
Wadannan yaran na kasar Morocco an yi masu masu ado ne a jajibarin sabuwar shekarar Amazigh ta 2,970

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Wadannan yaran na kasar Morocco an yi masu masu ado ne a jajibarin sabuwar shekarar Amazigh ta 2,970
Makada a babban birnin Morocco Rabat yayin da suke maraba da shigowa sabuwar shekarar Amazigh

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Makada a babban birnin Morocco Rabat yayin da suke maraba da shigowa sabuwar shekarar Amazigh
Ba kamar a Morocco ba, ana yin hutu ranar sabuwar shekarar a kasar Aljeriya, wadannan matan suke yin nasu a wani kauye da ke birnin Algiers.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Ba kamar a Morocco ba, ana yin hutu ranar sabuwar shekarar a kasar Aljeriya, wadannan matan suke yin nasu a wani kauye da ke birnin Algiers.
Tauraruwar fim 'yar Kenya Lupita Nyong'o kenan, yayin da take halartar taron Critics' Choice Awards a California na Amurka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tauraruwar fim 'yar Kenya Lupita Nyong'o kenan, yayin da take halartar taron Critics' Choice Awards a California na Amurka.
Presentational white space
Nan kuma masu tallan tufafi ne 'yan Afirka ta Kudu suke tallata hajarsu a birnin Berlin na Jamus

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Nan kuma masu tallan tufafi ne 'yan Afirka ta Kudu suke tallata hajarsu a birnin Berlin na Jamus.
Gidajen tallan tufafi a Afirka ta Kudu sun tanadi kayayyaki musamman saboda taron Mercedes-Benz Fashion Week.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gidajen tallan tufafi a Afirka ta Kudu sun tanadi kayayyaki musamman saboda taron Mercedes-Benz Fashion Week.
Makuei Puondak kenan, dan wasan kwallon kwando na tawagar Sudan ta Kudu yayin wasan da suke bugawa da kasar Somalia a Nairobin Kenya.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Makuei Puondak kenan, dan wasan kwallon kwando na tawagar Sudan ta Kudu yayin wasan da suke bugawa da kasar Somalia a Nairobin Kenya.
Wani mutum dauke da karensa a wata ambaliyar ruwa a babban birnin Angola wato Luanda ranar Juma'a.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum dauke da karensa a wata ambaliyar ruwa a babban birnin Angola wato Luanda ranar Juma'a.
Wani malami yana mayar wa da dalibai aikin da ya ba su a ajin makarantar da aka ga gawar wani yaro dan shekara 14 a birnin Abidjan na Ivory Coast.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani malami yana mayar wa da dalibai aikin da ya ba su a ajin makarantar da aka ga gawar wani yaro dan shekara 14 a birnin Abidjan na Ivory Coast.