Ranar Masu Nakasa Ta Duniya: 'Ba zan taba daina bara ba'

An wallafa

Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraren hirar Mustapha Musa Kaita da wasu masu larurar nakasa a Abuja

Tun a shekarar 1992 Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 3 ga watan Disamba domin ta zama Ranar Masu Nakasa Ta Duniya.

Sau da dama a Najeriya masu fama da larurar nakasa kan fada cikin halin bara a wani lokaci kuma wasu na kokarin yin sana'a domin neman na kansu.

A wannan dalili ne ya sa BBC ta tattauna da wasu nakasassu a garin Abuja domin jin ta bakinsu kan dalilinsu na bara, da kuma kuma irin kalubalen da suke fuskanta a matsayinsu na nakasassu.

Wani daga cikin masu larurar nakasa da BBC ta tattauna da shi mai suna Abubakar Mohammed ya shaida mana cewa a dalilin rashin samun sana'a ne ya sa yake bara.

Shi kuma Ibrahim Abubakar ya ce rashin samun tallafi a matsayinsa na nakasashe ya sa ya shiga bara.

Ya ce sau da dama a kauyuka idan an bayar da tallafi ba ya zuwa garesu.

Ya ce a haka ba za a hana su bara ba, a cewarsa, sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi a kan bara idan ba za a tallafa musu ba.

Ko a shekarar bara sai da nakasassun suka gudanar da wata zanga-zanga a majalisar dokokin Najeriyar, bisa rashin ba su kulawa ta musamman wajen daukar aiki.

Sun ce suna da masu ilimi da dama a cikinsu da za su iya yin duk wani aikin gwamnati.