Zamfara: An kama wanda ya mayar wa Gwamna Matawalle da martani

Asalin hoton, newsdigest.ng
Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta zargi gwamna Bello Matawalle da kama sakataren watsa labaranta saboda ya mayar masa da martani.
APC da ke adawa ta ce an kama Alhaji Ibrahim Dan Malikin Gidan Goga bayan gabatar masa da sammacin kotu kan zargin tunzura jama'a.
A ranar Juma'a ne gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle ya zargi tsohon gwamna Abdul'aziz Yari da hada baki da 'yan ta'adda don yi wa shirin zaman lafiyar da ya samar zagon kasa.
Shugaban kwamitin yada labarai na jam'iyyar APC a Zamfara, Ibrahim Muhammad Dan Madamin Birnin Magaji ya shaida wa BBC cewa suna tunanin kamen ba ya rasa nasaba da taron manema labarai da Dan Malikin Gidan Goga ya jagoranta inda ya mayarwa gwamna Matawalle da martani.
Ya ce 'yan sanda aka turo ranar Litinin daga gidan gwamnati da sammacin kama Dan Malikin Gidan Goga.
"Bayan Sallar Magariba yana masallaci ya fito suka ba shi takarda ya diba ya ga sammacin kama shi ne daga kotu."
"Ba su bari ya shiga gida ba, nan take suka tafi da shi," in ji shi.
Babu dai karin bayani daga rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, kuma BBC ta yi kokarin tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan amma sai ya kashe waya.
Dan Madamin Birnin Magaji ya ce sammacin ya nuna cewa a ranar Talata za a gabatar da Ibrahim Dan Malikin Gidan Goga a gaban babbar kotun shari'ar Musulunci tare da shi da tsohon shugaban karamar hukumar mulki ta Gusau.
Wannan dai wani alamu ne da wasu ke ganin zai jefa Zamfara cikin rikicin siyasa maimakon mayar da hankali ga kokarin kawo karshen kashe-kashen da aka shafe shekaru jihar na fuskanta.











