Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matar da ke sa mabiyanta na shafukan sada zumunta kamanta mutuwa
- Marubuci, Daga Lebo Diseko da Joanne Whalley
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
Gargadi: Wannan makalar na dauke da bayanan da ka iya tayar wa masu karatu hankali
Zanen wata doguwar mace mai dogon gashi ya dade rataye a gidansu. Amma Sara ba ta taba tunanin wani abu akai ba.
'Yarta Casey kwararriyar mai zane-zane ce tana daukar lokaci don nazarin abin da za ta zana.
Bayan dogon lokaci sai Sara ta fara tunanin akwai wani abu ga zanen kuma ta kudiri aniyar yin cikakken bincike. Ba a dade ba Casey ta lura wallafa zanen a internet.
A kasan hoton an rubuta; ''Wannan kyakkyawar matar ita ce Teal Swan, shahararriyar malamar duba.''
Wace ce wannan matar da ta zamo abar sha'awa ga matashiya 'yar shekara 18?
Teal Swan mace ce da ta ayyana kanta a matsayin malamar duba, kuma jagorar sauya juyin juya hali ta kashin kanta.
An haifeta a Utah a matsayin Mary Teal Bosworth, tana da mabiya a shafukan sada zumunta, kuma a shafinta ana kallon bidiyonta a Youtube sau miliyan 79.
Cibiyar da ta bude, mai ikirarin bai wa mutanen da suke cikin damuwa shawara, yawanci wadanda suka samu kansu cikin tsananin tashin hankalin da hankalinsu ke neman gushewa ko kokarin hallaka kai.
Ta yi imani da mutum na iya mutuwa kuma ya sake dawowa duniya, da karfin samar da waraka ga matsaloli, saboda a cewarta tana daya daga cikin wadanda suka tsira bayan yunkurin hallaka kanta, wannan ya ba ta kwarin gwiwar za ka iya gwada mutuwa kuma ka samu maganin matsalarka.
Swan ta ce manufarta ita ce taimaka wa wadanda suka samu kansu cikin tashin hankali, kuma yawancin mutanen sun ce koyarwarta ta taimaka musu kwarai da gaske.
Sai dai an fara zargin Swan tana kara sanya mutane cikin hadari musamman kan batun mutuwa, kuma masana halayyar dan adam sun fara kiran abin da take bai dace ba, kuma ba ya taimakawa sai sanya rayuwar mutane cikin hadari.
Sara ce zaune a falonta da ke arewa maso gabashin Amurka, tana sauraren wakokin ikilisiya yayin da hasken rana ya ratso tagar da ke falon.
Ita da mijinta sun shaida min cewa ta wayar tarho da aka kira su, aka fada musu labari mafi muni a rayuwa wato 'yarsu ta hallaka kanta.
Sara ta san 'yarta na fama da bacin ran rabuwar da suka yi da saurayinta, ba ta taba kawowa a ranta 'yarta za ta iya daukar mataki irin wanda ta dauka ba.
Sara ta fara duba shafukan sada zumunta da 'yarta ke amfani da su.
Ta gano Casey ta wallafa alkalami a shafinta na Facebook, a kasan shi ta rubuta Teal Swan, nan da nan ta gane 'yarta ta shiga kungiyar ''Teal Tribe'', kuma ba kowa iya shiga shafin ba sai idan kai mamba ne.
Sara ta yi shahadar kuda tare da shiga shafin, ta kadu matuka kan abin da ta gani.
Ta karanta wani sako da 'yarta ta wallafa cewa ta yi kokarin kashe kanta. Hoton da aka sanya a kasan sakon ya nuna wata mace da yatsunta biyu a goshi kamar bindiga.
An maida wa Caney martani ta hanyar sakwanni biyu daya daga ciki da ya taimaka wajen tura bidiyon Swan a jiki an rubuta: ''Ina son kashe kaina, abin da ya kamata ka yi idan za ka kashe kanka.''
A cikin bidiyon, malamar duba Swan ta bukaci wadanda suke son kashe kansu su tuntubi jami'an lafiya, amma sai ta ci gaba da cewa, ga wasu wannan matakin ba zai yi tasiri ba.
Ta kafe cewa hallaka kai tamkar ''shi ne abu mai sauki da yake kusa da mu za mu iya yin hakan a kowanne lokaci.''
Ta bayar da shawarar kallon bidiyon zai bai wa mutane damar jinge wannan a gefe guda, su mayar da hankali kan abin da ya kamata su dan samu nutsuwa.
Ta kuma bayar da misali da wani atisaye da masu kallon bidiyon za su gwada, inda ta kwanta a kasa ta saki jikinta kamar ta mutu, ta ce su kamanta su ne suka mutu.
Ta ce duk wanda ya gwada mutuwa zai fahimci babu abin da ya fi dadi kamar ka sake rayuwa... don me za ka tafi?
Ta ce kashe kai abu ne mai tayar da hankali, musamman ga masoyanka amma ba wani abu ba ne idan kana mace ko raye... ba ka son mutuwa, abin da kake bukata kawai shi ne ka fita daga halin kuncin da kake ciki.
Babu tabbas din ko Casey ba ta kalli bidiyon ba, amma idan dai ta kalla tabbas hakan ya taka rawa kan matakin kashe kanta da ta dauka.
Amma sakon da ta wallafa gabannin mutuwarta ya nuna wasu daga cikin kalaman da Swan da take yi, ciki har da sake haifar mutum bayan ya mutu.
Mahaifiyarta Sara ta fusata matuka da ganin bidiyon, tare da cewa shi ne kadai sakon da Casey ta wallafa a kungiyar Teal Tribe aka ba ta amsa, kuma babu wanda ya shaida wa 'yan sanda ko kuma yunkurin tuntubar iyayenta.
Ta wallafa sakon da makwanni biyu, kafin ta kashe kanta.
''Wannan babban kuskure ne da jefa rayuwar mutum cikin hadari,'' in ji Sara.
"Daman na yi tunanin akwai dalilin da ya sanya Casey kashe kanta, abin ya fi karfin tunanina, babu tantama kungiyar da Swan ke jagoranta ita ce ta bai wa 'yata karfin gwiwar kashe kanta.
"Babu wani abu da za a fada min da zai sauya min ra'ayina.''
"Tamkar fa an ba ta aiki ne ta yi atisayen yadda za ta kashe kanta," Sarah ta bayyana abin da bidiyon ya ke koyarwa.
Saboda kokarin gano ko akwai wani abu da ya kamata na kara sani, sai na shiga shafin Teal Tribe na Facebook, yana da mabobi sama da 27,000, anan na ci karo da tashin hankalin da ya wuce wanda na gani da farko.
A wannan shafi ana tattaunawa kan yadda mutum zai kashe kansa cikin sauki inda mutane da dama ke bayyana ra'ayinsu na son hallaka kansu, yayin da sauran mambobin kungiyar ke ba su kwarin gwiwa da karfafa musu gwiwar aikata hakan.
Sara ta ci karo da wasu shawarwari da aka zayyano da wanda ke son kashe kansa zai kaucewa don kar a samu kuskure. Amma dukkan bidiyon da ake nunawa a matsayin misali, jagora Swan ce ke aikatawa.
Makwannin da na dauka ina bibiyar abubuwan da ake tattaunawa da koyarwa a kungiyar, na gano matasa cikin mambobin kungiyar sun kashe kansu jim kadan bayan sanya bidiyon da yake koyarwar.
Koyarwa a zahiri
Baya ga koyarwa a shafin intanet, Swan ta kan shirya taruka a Amurka da Turai kan yadda za ka kashe kanka.
Tikitin shiga wannan abu dala 200 ne, na yi kokarin halartar daya daga cikin tarukan a birnin Chicago na ga dandazon matasa da suka halarci taron kuma a zahiri ake koyar da komai.
Wani ya shaida min Swan na sauya yadda duniya ke tafiya. Wani kuma ya ce min macen kwarai ce da ta san abin da ke faruwa da hanyoyin warware matsalolin rayuwa cikin sauki.
An dauki sa'a takwas a wajen taron, ana kuma kiran mambobin kungiyar da suke wajen su hau dandamali don Swan ta ba su shawara.
Suna tattaunawa a kan batutuwa masu muhimmanci a rayuwarsu, daga cin zarafi, zuwa sha'awaar hallaka kansu. Wani mutum ya ce a kowanne daren Allah yana kallon bidiyonta na sa'a biyar.
Bayan taron na samu ganawa da Swan, na kuma tambayeta shin me za ta ce wa wadanda suka zargeta da karfafa wa mutane gwiwar hallaka kansu?
Kawai sai ta bushe da dariya, kafin ta kada baki ta ce; ''wannan abin dariya ne, gaskiya abin dariya ne a gare ni.'' Sai kuma ta sha mur.
Ta ce bai dace a kira mabiyanta da masu hallaka kai ba, kuma duk wanda ya fadi hakan to bai taba kallon bidiyon da take wallafawa a shafin intanet ba.
Da na fada mata matasa biyu mambobin kungiyarta sun kashe kansu, sakamakon bidiyonta da suka kalla. Sai ta fara masifa.
''Ban san da su ba,'' ita ce amsar da ta ba ni.
Sai kuma ta kara fusata, fuskarta ta sauya launi zuwa ja-ja-ja, alamun bacin rai matuka, ta ce ai ita ce kuwa ke sauya wa mutanen da ke son kashe kansu tunani.
''Idan kika kalli yadda mutanen da suke sha'awar yadda nake magance musu matsaloli, za ki gane mutanen suna bukatar taimako.
''Idan kika ce wai ni, ina sa mutane na kashe kansu, ba maganar da hankali zai dauka ba ce.''
"Da na yi magana kan shafinta na Facebook, ta amince tana damuwa da hakan.
''Shi ne abin tayar da hankali kan abin da nake yi,'' ta shaida wa Sara.
''Kamar fa kin samar da wata kungiya ta shafin sada muzunta da zummar za ta zamo dandalin mutane masu ra'ayi irin naki.
"Mu ce mamba a dandalin ya yanke shawarar kashe kansa, don haka ba laifina ba ne daman tun kafin su shigo kungiyar suna fama da matsaloli.''
Amma ta amince wadanda suke taimaka wa wajen tafiyar da shafinta ba su da cikakken horon yadda abubuwan ke gudana, ba su san abin da za su yi ba idan suka ga wani ya wallafa sakon son hallaka kai.
Sara ta shaida mata shafukan sada zumunta ba su ne wuraren da ya kamata ta baje kolin koyarwarta ba.
"To ai ni ma ina yin wadannan tunanin na kashe kai a lokacin da nake shekara 15," in ji ta.
Bayan tattaunawar Sara da Swan, an samu sauyi don ta wallafa wani bidiyo a ciki ta fadi matsayarta kan yunkuri ko hallaka kai.
Swan ta bayyana karara ba ta amince da hakan ba, kuma ba ta goyon bayan masu yin hakan. Ta ce manufata ita ce taimaka wa wadanda suke cikin damuwa su samu sassaucin fita daga kangin da suka samu kansu a ciki amma ba hallaka kai.
Wannan mataki shi ne abin da wani kwararre kan halayyar dan adam ya shaida min a lokacin da nake gudanar da bincike.
Damuwar da kwararru suka nuna
Dukka sun nuna damuwa kan salon koyarwar Swan.
Daya daga cikin kwararrun mai suna Dr Jonathan Singer, shugaban kungiyar masu yaki da hallaka kai ta Amurka ne.
Ya ce: ''A lokacin da na samu labarin kungiyar Teal Tribe mai koyar da yadda mutum zai kashe kansa hankalina ya tashi.''
''Ana fadawa mabiya idan suka hallaka kansu, za su sake dawowa duniya ba tare da waccar matsalar da ta janyo suka dauki ransu ba.''
''Swan ita ce mai wannan tunanin kuma tana ganin hakan zai taimaka wa mutane, ta hanyar sanya musu tunanin su aikata hakan.''
Shi ma shugaban kungiyar yaki da hallaka kai ta Birtaniya Ged Flynn, ya yi tsokaci kan bidiyon Swan da na nuna masa.
''Gaskiya wannan ba ya taimakawa rage matsala sai ma karuwa da bullar wata sabuwar matsalar. Masu kokarin kashe kansu da sun ga bidiyon kakarsu ta yanke saka, sun samu gangara, wannan abu ne mai hadari ne.''
Dr Singer ya ce ya kamata kamfanonin sadarwa kamar su Facebook da Twitter su dinga kokarin shiga suna toshe "hauka" irin na Swan.
Har wa yau, wasu daga cikin mambobin kungiyar Teal Tribe sun kirkiri wata sabuwar kungiyar mai suna "Phoenix Tribe."
Ba kuma Teal Swan ke jagorantar ta ba, amma daya daga cikin manyan mabobinta ke tafiyar da shi. Kuma wasu daga cikin mambobi na yawan batun kashe kai, amma babu wanda ke cewa uffan don taimakawa ko bayar da shawara.
Da muka tuntubi Youtube matakin da suke dauka kan irin wadannan bidiyo? Sai suka ce suna kokarin daidaitawa tsakanin abin da mutane ke wallafawa.
Mutane na da damar tattauna abin da ke damunsu ko idan sun samu kansu cikin wani hali.