Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karnuka sun kashe wata mai ciki a Faransa
Karnuka sun kashe wata mai ciki a wani jeji da ke arewacin Faransa, yayin da ake farauta da karnukan a yankin, in ji masu bincike.
An gano gawar matar mai shekara 29 wadda take tafiya da nata karnukan a kusa da garin Villers-Cotterêts yayin da lamarin ya faru.
"Ta mutu ne sakamakon yawan cizon da karnukan suka yi mata a hannaye da kuma kanta," a cewar wani mai shigar da kara Frederic Trinh.
An gudanar da gwaje-gwaje kan karnuka 93 a wani kokari na gano wane kare ne cikinsu ya kai mata harin.
Cikin karnuka da aka yi wa gwajin har da na matar guda biyar.
Wani bincike da aka yi wa gawar matar ya nuna cewa ta mutu ne sakamakon cizon da karnukan suka yi mata a kai da hannaye.
'Yan sanda sun ce sun kaddamar da bincike kan kisan kai.
A cewar ofishin mai shigar da kara, matar ta yi wa mijinta waya cewar wasu gungun karnuka suna kokarin kai mata hari. Sai daga baya ya gano gawarta, bayan da ya yi ta jin kukan karnukanta.
Gungun karnukan da ta gani dai suna farautar gada ce, kamar yadda wata jaridar yankin Le Courrier Picard ta ruwaito.
Shugaban cibiyar kula da walwalar dabbobi na yankin Brigitte Bardot, ya yi kira ga hukumomin Faransa da su dakatar da farauta "har da wacce aka halatta a wannan kakar."
A wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Mafarauta ta Faransa ta ce "babu wata hujja da ke nuna cewa karnukan farauta ne suka yi ajalin matar."